Gwamnonin PDP Sun Saba da Atiku, Sun Yabawa Tinubu Kan Tsoma Baki a Rikicin Ribas
- PDP-GF ta yabi Bola Tinubu a kan yadda ya magance rikicin siyasar da ya kunno tsakanin Nyesom Wike da Gwamnan Ribas
- Kungiyar gwamnonin ta yi taron gaggawa a birnin Abuja a karkashin jagorancin Gwmanan Jihar Bauchi, Bala Mohammed
- Gwamna Bala Mohammed da abokan aikinsa sun kuma sallama cewa APC ta doke PDP a takarar shugaban Najeriya na 2023
Abuja - Kungiyar gwamnonin jihohin PDP ta yi taron gaggawa a ranar Litinin, a karshen zaman an yarda lokacin ajiye kayan yaki ya yi.
Shugaban gwamnonin PDP, Bala Mohammed ya yi wannan bayani da yake karanta jawabinsu, Vanguard ce ta fitar da wannan rahoto dazu.
"An kawo karshen siyasar 2023" - PDP-GF
Gwamna Bala Mohammed ya ce a sakamakon hukuncin da kotun koli ta zartar kan shari’ar zaben shugaban kasa, korafin zabe ya zo karshe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ko a makon nan Atiku Abubakar ya kira taron manema labarai, inda ya cigaba da yin Allah-wadai da hukuncin da alkalan kotun su ka zartar.
Rikicin Wike v Fubara a PDP
An yi zaman ne a gidan gwamnatin jihar Oyo da ke unguwar Asokoro a birnin Abuja. The Cable ta ce kungiyar ta hango karshen rikicin Ribas.
Gwamnan jihar Bauchi ya yi amfani da damar wajen kira ga takawaransu Simi Fubara da Nyesom Wike da su sasanta sabanin da su ka samu.
"Kungiyar ta tattauna a game da batutuwan da su ka dame ta, da jam’iyyar PDP da kuma kasa baki daya, kuma aka cin ma wadannan matsaya.
Gwamnonin PDP sun damu a kan abubuwan da su ke faruwa yanzu a jihar Ribas kuma su na maraba da tsoma bakin Mai girma shugaban kasa.
Taron ya yi kira ga duka bangarorin jihar Ribas su ajiye kayan yakinsu, a samu ayi sulhu.
Taron ya kuma yi la’akari da hukuncin kotun koli kan zaben 2023, wannan ya kawo karshen takarar shugaban kasa, dole akwai karshen shari’a."
- Bala Mohammed
APC ta karbi 'Yan NNPP da PDP
Ana da labari Abdullahi Umar Ganduje ya karbi ‘yan NNPP da su ka sauya shekar siyasa sun dawo APC mai mulki, a nan ya caccaki Kwankwasiyya.
‘Yan takaran Gwamna biyu da Shugabannin NNPP na kasa sun jefar da kwandon kayan marmari, Ganduje ya ce za a damu da su a APC mai-mulki.
Asali: Legit.ng