Shin da Gaske Wike Ya Bukaci Kaso 25 Na Kudin Shiga a Ribas? Babban Lauya Ya Magantu
- Yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin minista Wike da Gwamna Fubara, babban lauya ya fayyace komai
- Lauya kuma mai kare hakkin dan Adam, Chetam Thierry Nwala ya ce Wike shi ne ke da laifi a wannan rikici
- Ya ce Wike ne hi ya nada dukkan kwamishinonin Fubara da kuma hadimansa gaba daya a gwamnatin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ribas – Babban lauya kuma mai kare hakkin dan Adam ya bayyana ainihin dalilin da ya sa Nyesom Wike ke takun saka da Gwamna Sim Fubara na jihar Ribas.
Lauyan mai suna Chetam Thierry Nwala ya bayyana cewa Wike ya bukaci kaso 25 na kudin shiga a jihar inda Gwamna Fubara ya ki amincewa.
Mene lauya ke cewa kan rikicin Wike, Fubara?
Nwala ya bayyana haka ne a yau Talata 31 ga watan Oktoba yayin hira da gidan talabijin na Arise a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan ya ce Fubara ya nemi ragi inda ya bukaci ya rinka bai wa tsohon gwamnan kaso 10 daga ciki madadin kaso 25 da ya bukata.
Ya kara da Wike kusan shi ne ya nada dukkan kwamishinonin Fubara da hadimansa inda ya ce hatta babban mai tsaronshi, Wike ne ya nada shi.
Mene dalilin fadan Wike da Fubara a Ribas?
Ya ce:
“Abin da ya kamata mu fara magana akai shi ne, mene dalilin wannan matsalar, ko da na amince zan bi dokokinka akwai lokacin da za ka kure ni.
“Tun farko Wike ya bukaci kaso 25 na kudin shigar jihar, abin da mu ka ji shi ne Sim ya amince ya ba shi har kaso 10 daga arzikin Ribas.”
Ya ce dukkan kwamishinonin Sim, Wike ne ya nada hatta babban mai tsaron Fubara, Wike ne ya nada shi, kuma ayi tsammanin ba zai kure shi ba? Dole zai kure shi mana.
Fubara ya yi martani kan yunkurin tsige shi
A wani labarin, Gwamna Sim Fubara na jihar Ribas ya yi martani bayan yunkurin tsige shi a kujerar gwamna.
Fubara ya ce babu wani laifi da ya aikata da ya cancanci wannan cin mutunci daga majalisar dokokin jihar.
Asali: Legit.ng