Daga Karshe Wike Ya Yi Magana Kan Rikincinsa da Gwamna Fubara
- Nyesom Wike ya yi tsokaci kan rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Rivers, inda ya ce shugabannin jam'iyyar PDP sun shiga tsakani a rikicin
- Wike ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da gwamnonin PDP a masaukin gwamnan jihar Oyo da ke Abuja ranar Talata
- A ranar Talata ne Wike da Fubara suka gana a fadar shugaban ƙasa, inda aka ce shugaba Bola Tinubu ya sa baki kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya ce shugabannin jam'iyyar PDP sun shiga tsakani a rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Rivers.
Kamar yadda jaridar The Nation ta kawo rahoto, tsohon Gwamna Wike, shi ne ya bayyana hakan bayan ganawarsa da gwamnonin PDP a Abuja ranar Talata, 31 ga watan Oktoban 2023.
Wike ya bayyana cewa PDP ta karɓi ragamar komai kan rikicin kuma ba batun ƙabilanci ba ne kamar yadda ake zato.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da farko majalisar dokokin jihar Rivers ta gabatar da takardar shirin tsige gwamna Siminalayi Fubara a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba.
Tun da farko Wike da Gwamna Fubara sun gana a fadar shugaban ƙasa, inda Shugaba Tinubu ya shiga tsakani a rikicin da ya taso a tsakanin manyan ƴan siyasar biyu.
Gwamonin PDP sun gana kan Wike, Fubara
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya karɓi baƙuncin takwarorinsa gwamnonin jam'iyyar PDP domin tattauna batun tsige Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.
Taron wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP zai yi duba kan takun saƙan da ake yi a tsakanin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da magajinsa Gwamna Siminalayi Fubara.
Gwamna Fubara Ya Musanta Korar Manyan Hadimansa
A wani labarin na daban kuma, gwamnatin jihar Rivers a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Siminalayi Fubara, ta musanta rahotannin cewa gwamnan ya kori wasu daga cikin manyan hadimansa, saboda rikicinsa da Nyesom Wike.
A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar ya fitar, gwamnan ya buƙaci jama'a da su yi watsi da rahotannin da ake yaɗa wa kan batun korar shugaban ma'aikata, CSO da shugabannin ƙananan hukumomin jihar 23.
Asali: Legit.ng