Fubara, Makinde, Adeleke da Sauran Gwamnonin PDP Sun Gana Kan Shirin Tsige Gwamnan Rivers

Fubara, Makinde, Adeleke da Sauran Gwamnonin PDP Sun Gana Kan Shirin Tsige Gwamnan Rivers

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya karɓi baƙuncin manyan gwamnonin PDP a gidansa da ke birnin tarayya Abuja
  • Gwamnan ya karɓi baƙuncin gwamnonin ne domin tattaunawa kan batun dambarwar tsige Gwamna Fubara na jihar Rivers
  • Gwamnonin kuma za su tattauna kan batun zaɓukan gwamnan da ke tafe na jihohin Kogi, Bayelsa da Imo

FCT, Abuja - Gwamnonin jam’iyyar PDP sun isa masaukin gwamnan jihar Oyo da ke Abuja kan shirin tsige gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da majalisar dokokin jihar ta yi.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa ta yi kira da a gudanar da taron gaggawa ga dukkan mambobi da masu ruwa da tsaki a rikicin siyasar da ke faruwa a jihar Rivers domin a samu zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi wata hubbasa a rikicin siyasar Wike, Fubara

Gwamna Makinde ya gana da gwamnonin PDP
Makinde da sauran gwamnonin PDP sun gana kan batun tsige Gwamna Fubara Hoto: @OfficialPDPNigeria
Asali: Twitter

A ƙasa ga sunayen gwamnonin da suka isa taron gaggawan a masaukin Makinde:

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed; gwamnan jihar Plateau, Caleb Muftwang, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal da gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da: Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP na ƙasa ƙarƙashin jagorancin shugaban riƙo, Iliya Damagum.

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, da gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori sun halarci taron a Abuja.

Ƙungiyar gwamnonin PDP ƙarƙashin jagorancin Bala Mohammed, ana kuma sa ran za su tattauna kan zaɓukan da za a yi a jihohin Kogi, Bayelsa da Imo da rikicin siyasar jihar Rivers da sauran batutuwan da suka shafi jam’iyyar.

Tinubu ya shiga tsakani a rikicin Wike, Fubara

Kara karanta wannan

Fubara da Ministan Abuja sun haɗu a Aso Villa ana ƙishin-kishin ɗin Tsige Gwamnan PDP

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya shiga tsakani a rikicin siyasar da ya taso tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da magabacinsa Nyesom Wike.

Shugaba Tinubu ya buƙaci manyan ƴan siyasar biyu na jihar Rivers da su sasanta tsakaninsu domin samun zaman lafiya.

Gwamnonin PDP Sun Kira Taron Gaggawa

A baya rahoto ya zo cewa, ƙungiyar gwamnonin PDP ta kira taron gaggawa domin tattauna rikicin siyasar jihar Rivers.

Ana sa ran kungiyar gwamnonin ta duba sabanin da ake zargin an samu tsakanin takawaransu Similaye Fubara da kuma Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng