Shugaba Tinubu Ya Yi Wata Hubbasa a Rikicin Siyasar Wike, Fubara

Shugaba Tinubu Ya Yi Wata Hubbasa a Rikicin Siyasar Wike, Fubara

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani a rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Rivers
  • Shugaban ƙasar ya shiga tsakanin ne a rikicin da Gwamna Fubara da magabacinsa Nyesom Wike suke yi
  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, shi ne ya tabbatar da shiga tsakanin da shugaban ƙasar ya yi domin samun maslaha a rikicin

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani a cikin rikicin siyasa da tashe-tashen hankulan da suka addabi jihar Rivers.

A baya-bayan nan ne aka ruwaito cewa gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, da Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, na takun saƙa.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya kori shugaban ma'aikata, CSO da shugabannin LGA 23? Gwamnatin Rivers ta yi martani

Tinubu ya shiga tsakani a rikicin siyasar Rivers
Shugaba Tinubu ya gana da Wike, Fubara kan rikicin siyasar jihar Rivers Hoto: Nyesom Wike, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Wanda har hakan ya sanya majalisar dokokin jihar ta miƙa wa gwamnan takardar fara shirin tsige shi daga muƙaminsa, cewar rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu masana harkokin siyasa sun zargi Wike da laifin yunƙurin tsige gwamnan.

Mutane da dama dai na zargin ministan da kasancewa mai goyon bayan ƴan majalisar da ke kitsa yunƙurin tsige gwamnan.

Shugaba Tinubu ya shiga tsakani a rikicin Wike, Fubara

Amma a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, shugaba Tinubu ya yi amfani da damar taron majalisar ƴan sanda, wanda Wike da Fubara suka halarta domin shiga tsakani a rikicin da neman zaman lafiya a tsakanin manyan ƴan siyasar biyu.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana tsoma bakin da shugaban ƙasar yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan sakamakon taron ‘yan sandan da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa, Abuja.

Kara karanta wannan

Fubara da Ministan Abuja sun haɗu a Aso Villa ana ƙishin-kishin ɗin Tsige Gwamnan PDP

Duk da rashin jituwar da ke tsakaninsu, Gwamna Fubara da Wike sun gaisa a cikin wurin taron majalisar kafin a fara taron.

Muhammed wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP (PDP-GF) ya kuma bayyana cewa gwamnonin adawa sun ƙudiri aniyar yin aiki da shugaban ƙasa ne saboda ya nuna gaskiya ta hanyar rashin tsoma baki a shari’o’in gwamnonin da ƴan jam'iiyyar PDP suka gabatar a gaban kotu.

Gwamna Fubara Ya Musanta Korar Hadimansa

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Rivers a ƙarƙashin Gwamna Siminalayi Fubara ta musanta batun korar shugaban ma'aikatan gwamnan da shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Gwamnatin ta bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a rahotannin da ke cewa ta sallame su daga muƙamansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng