Gwamna Fubara Ya Kori Shugaban Ma'aikata, CSO da Shugabannin LGA 23? Gwamnatin Rivers Ta Yi Martani

Gwamna Fubara Ya Kori Shugaban Ma'aikata, CSO da Shugabannin LGA 23? Gwamnatin Rivers Ta Yi Martani

  • Gwamnatin jihar Rivers ta musanta rahoton cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya kori wasu manyan hadimansa
  • Waɗannan manyan hadiman sun haɗa da shugaban ma'aikatansa, babban jami'in tsaro (CSO) da dukkanin shugabannin ƙananan hukumomi
  • Wannan dai ya biyo bayan rashin jituwar da ake zargin an samu tsakanin gwamnan da kuma wanda ya gada, Nyesom Wike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Port Harcourt, jihar Rivers - A yayin da ake cigaba rigingimun siyasa a jihar Rivers a tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike, an yi zargin cewa gwamnan ya kori wasu manyan hadimansa.

Waɗanda aka yi zargin ya kora ɗin sun haɗa da sabon shugaban ma'aikatansa, babban jami’in tsaro (CSO) da kuma dukkanin shugabannin ƙananan hukumomin jihar.

Kara karanta wannan

Fubara da Ministan Abuja sun haɗu a Aso Villa ana ƙishin-kishin ɗin Tsige Gwamnan PDP

Gwamnatin Rivers ta musanta korar hadiman Gwamna Fubara
Gwamna Fubara ya musanta rahotannin korar shugaban ma'aikatansa da CSO Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Wannan zargin dai ya bayyana ne a wani rubutu da wani ɗan jarida ya yi a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoban 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rubutun na cewa:

"Na san akwai matsala lokacin da Siminalayi Fubara ya bayyana sunayen kwamishinonin Wike a matsayin kwamishinonin da za su yi aiki a ƙarƙashinsa."
"Korar da aka yi wa CSO da shugaban ma’aikata na nufin Fubara zai sarara sosai bayan wannan rigimar da ta faru a yau."
"Zaccheaus Adangor, wanda ya riƙe ma'aikatar shari'a a ƙarƙashin Wike, Dakotinama George-Kelly, ma'aikatar ayyuka, Isaac Kamalu, ma'aikatar kasafin kuɗi, da Chinedu Mmom, ma'aikatar ilmi na iya samun takardar kora nan ba da jimawa ba."

Gwamnatin Rivers ta mayar da martani

Dangane da waɗannan zarge-zargen, gwamnatin jihar Rivers ta musanta iƙirarin cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya kori wasu ma'aikata tare da ba da umarnin korar shugabannin ƙananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa a kan yunkurin tsige Gwamnan jihar Ribas

Kwamishinan yada labarai da sadarwa, Warisenibo Johnson, ya bayyana cewa gwamnan bai umarce shi da ya bayar da wannan sanarwar ba.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Johnson ya bayyana cewa:

“Mai girma gwamnanmu ƙwararre ne sosai a fannin aikin gwamnati, mai kirki kuma mutum ne mai mutuntawa wanda yake yin abubuwa bisa ƙa’ida da kuma tsoron Allah."
"Domin haka muna roƙon jama'ar Rivers da sauran jama’a da su yi watsi da irin waɗannan rahotannin da ba a tabbatar da su ba, domin za a sanar da jama'a kan wanda mai girma gwamna ka iya kora a lokacin da ya dace."
"Ya dace a lura cewa a matsayina na kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa, zan riƙa sanar da jama'a abubuwan da suka faru a kan lokaci."

An Fara Shirin Tsige Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, majalisar dokokin jihar Rivers ta aike da takardar fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara na jihar.

Majalisar dokokin ta fara shirin tsige gwamnan ne biyo bayan rahotannin cewa an samu saɓani tsakanin gwamnan da magabacinsa Nyesom Wike, ministan birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng