Kotun Koli: Sunayen Sanatoci da Jiga-Jigan PDP da Su Ka Yi Watsi da Jam’iyyar Bayan Faduwar Atiku

Kotun Koli: Sunayen Sanatoci da Jiga-Jigan PDP da Su Ka Yi Watsi da Jam’iyyar Bayan Faduwar Atiku

A ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba, kotun koli ta yanke hukunci inda ta kori karar dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar saboda rashin gamsassun hujjoji.

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Atiku da takwararshi na jam’iyyar LP, Peter Obi sun daukaka kara bayan rasa nasara a kotun kararrakin zaben a wata Satumba.

Jerin sanatoci da jiga-jigan jam'iyyar PDP da su ka yi murabus bayan hukuncin kotun koli
Jam'iyyar PDP ta samu matsala tun bayan hukuncin kotun koli. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Facebook

Tun farko, kotun saurararan kararrakin zaben ta yi fatali da korafe-korafensu inda ta ce kwata-kwata babu hujjoji gamsassu.

Bayan rashin nasarar Atiku a kotun koli, da alamu jam’iyyar ta fara samun matsala inda jiga-jigan jam’iyyar su ka rinka ficewa wasu kuma na murabus.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanaki uku kacal da hukuncin, sanatoci biyu da tsohon mamban majalisar Tarayya da wasu jiga-jigan jam’iyyar sun fice daga PDP.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jigon Jam’iyyar PDP a Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Jam’iyyar Ta Shiga Dimuwa

Legit Hausa ta tattaro muku jerin jiga-jigan PDP da su ka tsere bayan hukuncin:

1. Sanata Ayo Akinyere daga Ondo

Sanata Ayo daga jihar Ondo ya jagoranci mambobin jam’iyyar fiye da 2000 zuwa jam’iyyar APC bayan ya yi murabus daga jam’iyyar.

Wannan babbar matsala ga jam’iyyar PDP wanda ya kamata su dauki tsauraran matakai don shawo kan matsalar da gaggawa.

2. Sanata Obinna Ogba daga Ebonyi

Jam’iyyar ta sake samun gagarumar matsala bayan Sanata Obinna daga jihar Ebonyi ya yi murabus a jam’iyyar inda ya ke godiya ga jam’iyyun adawa da su ka taimaki siyasarshi.

Ogba ya wakilci Ebonyi ta tsakiya tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023, ya yi murabus a ranar Juma’a 27 ga watan Oktoba kwana daya bayan hukuncin kotun koli.

3. Livinus Makwe daga Ebonyi

Tsohon mamban majalisar Tarayya, Makwe da sauran jiga-jigan PDP sun watsar da kashin jam’iyyar bayan yanke hkuncin kotun koli.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Bayan Shan Kaye a Kotun Koli, Shugaban LP na Kasa Ya Sallami Hadimansa 5

Makwae ya wakilci mazabar Ohaozora/Onicha da Ivo daga shekarar 2019 zuwa 2023.

4. Shugabannin PDP a kananan hukumomi shida

Akalla shugabannin jam’iyyar PDP a kananan hukumomi shida ne su ka yi murabus bayan yanke hukuncin kotu a jihar Ebonyi wadanda su ka hada da:

i. Agbom Friday – karamar hukumar Ezza ta Kudu

ii. Nwofe Philip Don – karamar hukumar Izzi

iii. Nwobasi Ude – karamar hukumar Ohaozara

iv. Chukwu Michael – karamar hukumar Ivo

v. Ifere Sunday – karamar hukumar Ikwo

vi. Ndukwe Orji – karamar hukumar Afikpo ta Kudu

5. Sauran jiga-jigan PDP da su ka yi murabus a Ebonyi

Matsalar ta PDP ta kuma shafi sauran manyan jam’iyyar a jihar wanda jiga-jigan jam’iyyar da ake ji da su a jihar su ka yi murabus, sun hada da:

i. James Alaka – sakataren tsare-tsare

ii. Ebeh Kingsley – shugaban matasa na yanki

iii. Uchenna Nwafor – tsohon mai bincike na yanki

Kara karanta wannan

"Dole Sai Gwauro": NDA Ta Fitar da Tsarin Dibar Sabbin Dalibai Karo Na 76, Ta Bayyana Ka’idojin Cikewa

iv. Samuel Onyeleke – shugaban matasa na Ebonyi ta Arewa

Atiku ya yi martani kan hukuncin kotun koli

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi martani a karon farko kan hukuncin kotun koli.

Atiku ya ce kotun kolin ta zubar da mutuncinta wurin halasta haram da takardun bogi yayin hukuncin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.