Shugaba Tinubu Ya Ware Wa INEC Naira Biliyan 18 Na Zabukan Gwamnonin Jihohi 3
- Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tinubu ta amince a sakarwa hukumar INEC da naira biliyan 18 don gudanar da zaben watan Nuwamba
- Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu ne ya tabbatar da haka a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba
- A cewar Bagudu, hukumar zaben za ta samu kudin ne daga cikin karin tiriliyan 2.1 na kasafin kudin shekarar 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullun
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ware wa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INECC) naira biliyan 18 don gudanar da zabukan gwamnonin Bayelsa, Imo da Kogi wanda za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023.
Dalilin da yasa Tinubu ya amince da biliyan 18 don zabukan Nuwamba, minista ya magantu
Shugaba Tinubu ya amince da ƙarin Naira tiriliyan 2.18 a kasafin kuɗin 2023, ya faɗi ayyukan da za a yi
A cewar ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu, INEC za ta samu kudin ne daga cikin karin naira tiriliyan 2.1 (N2,176,791,286,033) na kasafin kudin 2023, jaridar The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bagudu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba, a fadar shugaban kada da ke Abuja, bayan taron majalizar zartarwa wanda aka yi a ranar, Channels TV ta rahoto.
“Hakazalika, an ware naira biliyan 18 ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta don tallafa musu wajen gudanar da zabukan Bayelsa, Kogi da Imo,” in ji shi.
A cewarsa, an amince da karin kasafin kudin ne don magance matsalolin gaggawa.
Tinubu ya nada kwamishinonin zabe 9
Legit Hausa ta rahoto a baya cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada sabbin kwamishinonin zabe a jihohi tara a Najeriya.
Tinubu ya yi nadin ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabukan jihohi a Kogi da Imo da Bayelsa a watan Nuwamban wannan shekara, Legit ta tattaro.
Hadimin shugaban a bangaren yada labarai ta zamani, David Olusegun shi ya bayyana haka a shafinsa na Twitter a yau Laraba 25 ga watan Oktoba.
Daga cikin wadanda aka nada akwai Mista Isah Shaka Ehimeakne - Kwamishinan zaben jihar Edo da Mista Bamidele Agbede — Kwamishinan zaben jihar Ekiti.
Asali: Legit.ng