Barazanar Tsige Akpabio: Na Fi Shi Kwarewa a Harkalla, Ndume Ya Kalubalanci Shugaban Majalisar

Barazanar Tsige Akpabio: Na Fi Shi Kwarewa a Harkalla, Ndume Ya Kalubalanci Shugaban Majalisar

  • Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume ya bayyana yadda ta kaya tsakaninsa da shugaban majalisar, Godswill Akpabio
  • Ndume ya ce ya sani ya fi Akpabio kwarewa a sanin harkar majalisar inda ya ce kuma ya na daya daga cikin wadanda su ka yi wa masa kamfe
  • Sanatan ya bayyana haka a yau Litinin 30 ga watan Oktoba a Abuja yayin hira da gidan talabijin na Channels

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Sanata Ali Ndume ya ce ko kusa shi ba sa’an shugaban majalisa, Godswill Akpabio ba ne a sanin harkallar majalisar, Legit ta tattaro.

Sanatan wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels TV.

Kara karanta wannan

Atiku: Kotun koli ta halasta haram da kirkirar takardar bogi

Ndume ya kalubalanci Akpabio, ya ce ya fishi kwarewa a harkokin majalisar
Ndume ya kalubalanci Akpabio kan shugabancin Akpabio. Hoto: Nigeria, Sen. Muhammad Ali Ndume.
Asali: Facebook

Mene Ndume ya ce kan Akpabio game da majalisar?

Yayin da ya ke bayani kan salon mulkin Akpabio, Ndume ya ce matsalarshi daya yadda Akpabio ya ke gudanar da salon mulkinsa a majalisar, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Yadda ya ke gudanar da salon mulkinsa abin takaici ne, abin da ya faru a baya an yi wa abin mummunan fahimta, kada ku manta ni na yi wa Akpabio kamfe don a zabe shi.
“Ba zai yiyu ka gina gida kuma ka rusa shi ba, matsalar ita ce na fishi kwarewa a harkar majalisa, duk lokacin da na so yi masa gyara, bai kamata ya nunamin iko ba, ya kamata ina masa gyara.”

Wane shawari Ndume ya bai wa Akpabio?

Ndume ya ce ya kamata a wancan lokacin Akpabio ya gayyace shi su yi magana su kadai amma bai yi ba, shi kuma zai tafi sallah lokacin karfe 12:30 na rana ce.

Kara karanta wannan

Rivers: 'Ban Aikata Laifin da Zai Sa a Tsige Ni Ba', Fubara Ya Yi Martani Kan Yunkurin Kifar Da Shi

Idan ba ku manta ba, Ndume ya fice daga dakin majalisar a ranar 19 ga watan Oktoba bayan hatsaniya da shugaban majalisar, Godswill Akpabio.

Majalisar Dattawa ta kare matakin siyan motocin alfarma

A wani labarin, Majalisar Dattawa ta kare matakinta na karbar motocin alfarma da ake ta cece-kuce a kansu a ‘yan kwanakin nan.

Majalisar ta ce ai akwai wasu ministoci da ke da manyan motoci ma su tsada fiye da guda uku amma ba a magana.

Wannan na zuwa ne yayin da majalisun Tarayya su ka shirya karbar motocin alfarma ma su tsadar gaske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.