Atiku: Kotun Koli Ta Halasta Haram da Kirkirar Takardan Bogi
- Dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya yi kakkausar suka ga hukuncin kotun koli da aka yi a makon da ya gabata
- Atiku ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a yau Litinin 30 ga watan Oktoba inda ya ce babu adalci kwata-kwata
- Ya ce idan har kotun koli wacce ita ce a sama za ta halasta laifukan da su ka shafi coke da almundahana da satar kamanni, to akwai matsala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya soki yadda hukuncin kotun koli ya kasance a makon da ya gabata.
Atiku ya bayyana cewa hukuncin da kotun ta yanke ya tabbatar da cewa ta na goyon bayan rashin bin doka da almundahana da kuma aikata haram, Premium Times ta tattaro.
Mene Atiku ke cewa kan kotun koli?
Dan takarar ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a yau Litinin 30 ga watan Oktoba a Abuja a karon farko tun bayan hukuncin kotun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Wani ya tambaye ni, wai meye zan yi idan na rasa nasara a kotun koli.
“Na ba shi amsa da cewa idan dai Najeriya ta yi nasara, da gwagwarmayar ta duniya ce baki daya.
“Ina nufin, nasarar ta Najeriya ce ba ta wa ba idan kotun koli ta halasta almundahana da coke da satar kamanni kamar yadda ta yi.”
Wane tabbaci Atiku ya bayar?
Atiku ya kara da cewa idan har babbar kotun kasar ta tabbatar da laifi a matsayin abu mai kyau kuma har da kyauta, to Najeriya ta bata hanya, cewar TheCable.
Ya ce ya na da tabbacin tarihi zai tabbatar da gaskiyarsa a cikin wannan gwagwarmaya da ya ke yi.
Atiku ya kalubalanci zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Faburairun wannan shekara da mu ke ciki.
Kotun koli yayin hukuncinta, ta tabbatar da Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.
'Babu in da zan je', Atiku ya magantu kan kotun koli
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce duk da rashin nasara a kotun koli, babu in da zai je.
Atiku ya ce zai ci gaba da gwagwarmayar nema wa 'yan Najeriya hakkinsu da aka siyar a kotun koli.
Wannan na zuwa ne bayan kotun koli ta yanke hukuncin zaben shugaban kasa a ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng