Bayan Shan Kaye a Kotun Koli, Shugaban LP na Kasa Ya Sallami Hadimansa 5

Bayan Shan Kaye a Kotun Koli, Shugaban LP na Kasa Ya Sallami Hadimansa 5

  • Kwanaki biyu bayan shan kaye a kotun koli, jam’iyyar LP ta salami wasu daga cikin mukarraban jam’iyyar da su ka ba da gudunmawa
  • Shugaban jam’iyyar, Barista Julius Abure shi ya sanar da korar wasu daga cikin hadimansa da su ka ba shi gudunmawa a tafiyar
  • Wannan na zuwa ne bayan kotun koli ta yi fatali da korafe-korafen jam’iyyun adawa da su ka hada da PDP da LP da sauransu

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Shugaban jam’iyyar LP, Barista Julius Abure ya fatattaki wasu daga cikin hadimansa

Abure ya dauki wannan matakin ne kwanaki biyu bayan jam’iyyar ta sha kaye a kotun koli da ta bai wa Tinubu nasara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jigon Jam’iyyar PDP a Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Jam’iyyar Ta Shiga Dimuwa

Shugaban jam'iyyar LP, Abure ya sallami hadimansa bayan faduwa a kotun koli
Shugaban Jam’iyyar LP, Julius Abure ya sallami hadimansa. Hoto: Labour Party.
Asali: UGC

Wane hukunci Abure ya dauka kan hadimansa?

A cikin wata sanarwa da sakataren jam'iyyar ya fitar, Malam Farouk Umar ya ce dukkan nade-nade da aka yi tun daga kamfe har zabe an rusa su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“Wadanda korar ta shafa sun hada da Mista Mandela Ukegbu, shugaban kamfe na shugaban kasa da Injiniya Balami Isaac da Didacus Joe-Adigwe.
"Sauran sun hada da Princess Ajibola, hadimar shugaban a ayyuka na musamman da Isaac Imasuagbon, hadimin shugaban a bangaren sadarwa ta zamani da sauransu.”

Wane fata Abure ya yi wa hadimansa?

Abure ya musu fatan alkairi yayin da su ke ci gaba da rasuwarsu a sauran bangarori na rayuwa, Daily Trust ta tattaro.

Bayan hukuncin kotun koli, jam’iyyar ta yi fatali tare da kin amincewa da hukuncin kotun da cewa akwai rashin adalci.

Kara karanta wannan

Isra’ila da Falasdinu: Kungiyar Shi’a Ta Tura Gargadi Mai Kama Hankali Ga Tinubu Kan Ta’addancin Isra’ila

Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na LP sun kalubanci sahihancin zaben Tinubu da su ka yi zargin akwai kura-kurai a ciki.

Har ila yau, jam’iyyun adawan sun kara shan kaye bayan fatali da korafe-korafensu, inda kotun ta kuma tabbatar da Tinubu a matsayin shugaban kasa.

Kotun koli ta yi fatali da korafe-korafen PDP, LP

A wani labarin, kotun koli a Abuja ta yi fatali da karar jam’iyyun adawa da su ka hada da PDP da LP.

Kotun ta kuma tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a matsayin halastacce kuma zababben shugaban kasa.

Atiku Abubakar da Peter Obi na kalubalantar zaben Tinubu na jam’iyyar APC da aka gudanar a watan Faburairu na wannan shekara da mu ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.