Gwamnan PDP Da Ya Ziyarci Tinubu Bayan Kotu Ta Yanke Hukunci Ya Fadi Dalilin Ziyarsa

Gwamnan PDP Da Ya Ziyarci Tinubu Bayan Kotu Ta Yanke Hukunci Ya Fadi Dalilin Ziyarsa

  • Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya yi martani ga caccakar da ya sha kan ziyartan Shugaban kasa Bola Tinubu bayan hukuncin kotun koli
  • An gano Diri, wanda ya kasance jigon jam'iyyar adawa a wani bidiyo da ya yadu yana taya shugaban kasar murna a ofishinsa tare da sauran manyan yan siyasa
  • Gwamnan na Bayelsa ya bayyana cewa yanada yancin taya shugaban kasar Najeriyan murna

Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya magantu a kan ziyarar da ya kai wa shugaban kasa Bola Tinubu a kwanan nan, yana mai cewa ba sabon abu bane.

A yayin ziyarar da ya kai garin Igbedi da ke karamar hukumar Kolokuma/Opokuma na jihar daga cikin kamfen din gwamnan na PDP, Gwamna Diri ya yi bayanin cewa yana da yancin taya Shugaban kasa Tinubu murna kan hukuncin kotun koli akan zaben shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Ana Min Kallon Ba Zan Iya Ba Saboda Na Iya Rawa, Gwamnan PDP

Douye Diri ya ce yana da yancin taya Tinubu murnar nasara a kotun koli
Gwamnan PDP Da Ya Ziyarci Tinubu Bayan Kotu Ta Yanke Hukunci Ya Fadi Dalilin Ziyarsa Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, ya ce:

"Jiya (Alhamis), na kasance a Abuja, kuma yawancinku kun ga bidiyon da ke yawo. Yanzu yan adawa sun tashi tsaye suna karairayi. Shakka babu, wannan ne dabi'arsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A matsayin gwamna mai ci, akwai shugaban kasa mai ci, kuma babu wanda ke bina bashin rantsuwa game da ziyarar da na kai wa shugaban kasar."

Ya yi karin haske cewa ziyarar da ya kai fadar villa don tattauna muhimman batutuwan jihar tare da shugaban kasar ne, kuma tattaunawar tasu ta yi amfani.

Gwamna Diri ya yi watsi da jita-jita da ikirari na ’yan adawa ke yi, inda ya nuna cewa ziyarar tasa ba ta sanyaya su ba.

Zaben Bayelsa: Gwamna Diri ya soki dan takarar APC da aka tsige

Ya kuma jaddada cewar dan takarar APC a zaben gwamna mai zuwa yana nan a matsayin wanda aka tsige, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta gyara a bangarenta.

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Babban Mai Adawa Da Buhari Ya Taya Tinubu Murna, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Atiku

Ya karfafawa masu kada kuri'u a Bayelsa da kada su yi asarar kuri'unsu kan jam'iyyar da bata kan takardar zabe.

Ortom ya taya Tinubu murna nasara

A wani labarin, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya shiga sahun masu taya shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu murna kan tabbatar da nasarar zabensa da kotun koli ta yi.

Ya nanata cewa hukuncin kotun kolin babban nasara ce ga damokradiyya da yancin cin gashin kan cibiyoyin dimokaradiyyar kasar, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel