Jonathan Ya Ziyarci Tinubu a Fadarsa Bayan Nasara a Kotun Koli, an Yada Bidiyon

Jonathan Ya Ziyarci Tinubu a Fadarsa Bayan Nasara a Kotun Koli, an Yada Bidiyon

  • Tsohon shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya kai ziyarar bazata fadar shugaban kasa da ke birnin Tarayya, Abuja
  • A cikin wani faifan bidiyo, an gano tsohon shugaban ya na taya Shugaba Tinubu murnan samun nasara a hukuncin kotun koli
  • Goodluck ya janye jikinsa a harkokin siyasa a shekarar 2020 kuma tuni ya zama dattijo a kasar tun bayan barin shi kujerar mulki

FCT, Abuja – Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya ziyarci Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan kotun koli ta yanke hukuncin shari’ar zaben shugaban kasa a jiya Alhamis 26 ga watan Oktoba, Legit ta tattaro.

Jonathan ya kai ziyarar murnar samun nasarar da Tinubu ya yi a kotun zabe
Jonathan Ya Ziyarci Tinubu a Fadarsa. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Meye dalilin ziyarar da Jonathan ya kai wa Tinubu?

A cikin wani faifan bidiyo da gidan talabijin ta NTA ta wallafa a shafin Twitter, an jiyo Jonathan na taya Shugaba Tinubu murnar yin nasara a kotu.

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Babban Mai Adawa Da Buhari Ya Taya Tinubu Murna, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Atiku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya samu nasara a kotun koli a jiya Alhamis 26 ga watan Oktoba inda ya yi doke abokan hamayyarsa na jam’iyyun PDP da LP.

Atiku da Obi sun daukaka kara bayan kotun zabe ta yi fatali da korafin da su ka shigar gabanta a watan Satumba.

Tun farko sun kalubalanci zaben Tinubu a matsayin shugaban kasa a jam'iyyar APC a watan Faburairu na wannan shekara.

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu kan wannan ziyara:

Hayatu Aminu ya ce alamun dan kasa nagari kenan, mai son ci gaban Nigeria da al'ummarta gaba daya tabbas mun ji dadi a mulkinsa.

Salisu Ladan ya ce:

"Gaskiya Jonathan mutumin kirki ne mun shaida haka, musamman a mulkinsa."

Aminu Abubakar ya ce ai ba don Allah ya je ba, ya je ne nemo dukiyarsu ce da Buhari ya kwace a mulkinsa.

Kara karanta wannan

“Dadina Da Gobe Saurin Zuwa”: Kalaman Mawaki Rarara Sun Tayar da Kura a Tsakanin Yan Najeriya

Ganduje ya taya Tinubu murnar nasara a kotun zabe

A wani labarin, shugaban jam'iyyar APC, Dakta Umar Ganduje ya taya Shugaba Tinubu murnar yin nasara a kotun zabe.

Ganduje ya ce wannan nasara ta 'yan Najeriya ce gaba daya inda ya bukaci a bai wa Tinubu hadin kai don gina kasa.

Ya kuma shawarci Atiku da Obi su yi hakuri har sai zuwa 2031 su sake gwada sa'arsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.