Hukuncin Kotun Koli: Ganduje Ya Bayyana Shekarar da Atiku, Peter Obi Za Su Yi Takarar Shugaban Kasa
- A ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba ne kotun koli ta yi fatali da shari'ar Peter Obi da Atiku kan Bola Tinubu saboda rashin hujjoji
- Babbar kotun ta kuma ayyana Tinubu a matsayin ainahin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023
- Bayan hukuncin da kotu ta yanke, shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya bukaci abokan hamayyar Tinubu da su jira 2031 don takarar kujerar shugaban kasa
FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya bukaci dan takarar PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na LP, Peter Obi da su jira zuwa 2031 domin cimma kudirinsu na son zama shugaban kasa Bayan cikar wa'adin mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba biyu.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, yayin da yake jinjinawa hukuncin kotun koli wanda ya tabbatar da nasarar Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Ganduje ya bayyana a cikin wata sanarwa daga hadiminsa, Edwin Olofu, cewa hukuncin ya kawo karshen dukkanin ikirarin da jam'iyyun adawa ke yi na cewa an yi magudi a zaben shugaban kasar don Tinubu ya yi nasara, jaridar Punch ta rahoto.
Ya bayyana cewa sakamakon hukuncin kotun kolin zai bayar da damar da Tinubu zai mayar da hankalinsa kan muhimmin aikin kasa, Channels TV ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jiga-jigan siyasa sun cika da murna
Idan da rai da lafiya kuma aka cigaba da tafiya a haka, Bola Ahmed Tinubu ne shugaban Najeriya akalla har zuwa Mayun 2027.
Mun dai ji cewa magoya baya da shugabannin APC har da Muhammadu Buhari sun yi maraba da sakamakon da alkalan kotun koli su ka yi a jiya.
Obi ba zai shugabanci Najeriya ba, Reno
A wani labarin, mun ji cewa mai sukar siyasa kuma mai sharhi kan al'amuran jama'a, Reno Omokri ya mayar da martani kan hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar da nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Omokri ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba.
Ya bayyana wannan ne jim kadan bayan kotun koli ta yanke hukuncinta na karshe kan zaben shugaban kasa na 2023.
Asali: Legit.ng