Shari’ar Zabe: “Ku Yi Hakuri Zuwa 2031”, Ganduje Ya Tura Muhimmin Sako Ga Atiku, Obi

Shari’ar Zabe: “Ku Yi Hakuri Zuwa 2031”, Ganduje Ya Tura Muhimmin Sako Ga Atiku, Obi

  • Abdullahi Ganduje, shugaban jam’iyyar APC ya taya Shugaba Tinubu murnar nasara a kotun koli
  • Ganduje ya yi kira ga Atiku da Obi da su yi hakuri su jira bayan Tinubu ya kammala mulkinsa a 2031
  • Ya nemi hadin kan ‘yan Najeriya da su goyin bayan Tinubu don ganin ya inganta rayuwar ‘yan kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja – Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Ganduje ya yi martani bayan hukuncin kotun koli.

Kotun koli ta tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a yau Alhamis 26 ga watan Oktoba inda ta yi fatali da sauran ‘yan takara.

Ganduje ya taya Tinubu murnar nasara, ya tura sako ga Atiku, Obi
Ganduje ya yi martani kan hukuncin kotun koli. Hoto: Bola Tinubu, Abdullahi Ganduje.
Asali: Twitter

Meye Ganduje ke cewa kan hukuncin kotun koli?

A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na Ganduje, Edwin Olofu ya fitar, ya bukaci Atiku Abubakar da Peter Obi da su jira shekakar 2031.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan PDP 4 da Su ka Nuna Farin Ciki da Nasarar Tinubu Kan Atiku a Kotun Koli

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gandue ya ce wannan nasara ta Tinubu ya tabbatar da cewa zaben da aka gudanar babu almundahana kamar yadda ake zargi, cewar Leadership.

Daga bisani ya taya shugaban murnar nasara inda ya tabbatar da cewa hukuncin ya kwance dukkan zargin da ‘yan adawa ke yi kan zaben Tinubu.

Wane shawara Ganduje ya bai wa Obi da Atiku?

Ya ce:

“Najeriya ta mu ce gaba dayanmu, dole ne mu hada kai don ciyar da kasar gaba a matsayinmu na ma su kishin kasa.
“Ina ta ya Atiku da Peter Obi murnar dagewa don ganin sun samu mafita wanda hakan ya karawa dimukradiyya karfi.
“Wannan dimukradiyya ce, nasarar Tinubu nasara ce ga dimukradiyya, har yanzu akwai dama ga Atiku da Obi su gwada sa’arsu bayan Tinubu ya gama a 2031.”

Ganduje ya kirayi Atiku da Obi da su cire duk wata gaba don barin Tinubu ya ci aba da aikin alkairi a kasar don karuwar ‘yan Najeriya, TVC News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Abun Mamaki: Gwamnan PDP Ya Je Villa Tare da Ƙusoshin APC, Ya Taya Tinubu Murnar Nasara a Kotu

Ya kuma kirayi ‘yan Najeriya da su goyi bayan Tinubu a kokarinsa na ganin ya inganta rayuwar al’ummar kasar.

Kotu koli ta yi fatali da sabbin korafe-korafen Atiku

A wani labarin, Kotun koli a yau Alhamis 26 ga watan Oktoba ta ce ba za ta bata lokacinta ba wurin sake karbar sabbin korafe-korafen Atiku Abubakar.

Kotun ta ce wannan kokari na Atiku zai tsawaita hukuncin kotun wanda kuma baya ne a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.