"Peter Obi Ba Zai Taba Zama Shugaban Kasar Najeriya Ba": Inji Reno Omokri Bayan Hukuncin Kotun Koli

"Peter Obi Ba Zai Taba Zama Shugaban Kasar Najeriya Ba": Inji Reno Omokri Bayan Hukuncin Kotun Koli

  • Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya cika da murna kan faduwar Peter Obi a kotun koli
  • Omokri ya ce Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba
  • Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X yayin da yake rawar wata waka mai suna "The Obito Continua"

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Mai sukar siyasa kuma mai sharhi kan al'amuran jama'a, Reno Omokri ya mayar da martani kan hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar da nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Omokri ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba.

Reno Omokri ya ce Peter Obi ba zai taba zama shugaban kasa ba
"Peter Obi Ba Zai Taba Zama Shugaban Kasar Najeriya Ba": Inji Reno Omokri Bayan Hukuncin Kotun Koli Hoto: Reno Omokri/Mr Peter Obi
Asali: Facebook

Ya bayyana wannan ne jim kadan bayan kotun koli ta yanke hukuncinta na karshe kan zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Tinubu a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter a baya, @renoomokri, an gano tsohon hadimin tsohon shugaban kasar yana rawar wata waka mai taken "The Obito Continua".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta rahoto cewa kotun koli ta tabbatar da nasarar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Da take zartar da hukunci a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, kotun ta bayyana cewa karar da Atiku Abubakar, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya shigar bata da inganci, jaridar The Cable ta rahoto.

"Ku kalle ni ina rawar The Obito Continua. Peter Obi BA ZAI TABA zama shugaban kasar Najeriya ba!"

Reno na so Tinubu ya binciki Buhari

A wani labarin, mun ji a baya cewa Reno Omokri, mai taimakawa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya bayyana yadda tattalin arzikin Najeriya ya durkushe a ƙarƙashin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Alkalin Alkalai Ariwoola Ya Amince a Haska Hukuncin Kotun Koli Kai Tsaye

Jigon a jam'iyyar PDP a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Asabar, 21 ga watan Oktoba, ya yi iƙirarin cewa Buhari ya lalata kuɗin Najeriya tare da shirin tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar.

Ya yi nuni da cewa rikicin siyasar Nijar ya sa Buhari ya sauya shawara inda a ƙarshe ya yi ritaya zuwa jiharsa ta Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng