Shari’ar Zabe: Tinubu Ya Yi Martani Bayan Nasara Kan Atiku a Kotu, Ya Tura Muhimmin Sako
- Shugaba Tinubu ya bayyana jin dadinsa bayan samun nasara a kotun koli na zaben shugaban kasa da aka yanke hukunci a yau
- Tinubu ya yabi bangaren shari’a wurin tabbatar da gaskiya ba tare da tsoro ko kuma son kai yayin yanke wannan hukunci
- Ya bukaci sauran ‘yan takara da jama’ar Najeriya baki daya da su zo su gina kasar inda ya ce yanzu lokacin kawo ci gaba ne a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi martani bayan samun nasara a kotun koli a yau Alhamis 26 ga watan Oktoba.
A yau ne kotun koli ta tabbatar da Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa bayan korar korafe-korafen Atiku Abubakar da Peter Obi.
Meye Tinubu ya ce bayan hukuncin kotu?
Tinubu ya ce lokaci ya yi da ya kamata a taru a gina kasar Najeriya tun da shari’ar zabe ta kare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ya bayyana haka ne jim kadan bayan yanke hukuncin zaben shugaban kasa da aka dade ana yi.
Ya ce kotu ta yi hukunci na adalci game da dukkan korafe-korafe ba tare da son kai ko kuma nuna tsoro ba yayin hukucin.
Wane kira Tinubu ya yi wa Atiku, Obi?
A cewarsa:
“Na karbi wannan hukunci da hannu biyu wanda Mai Shari’a John Okoro ya jagoranta bayan korafi daga jam’iyyun PDP da LP na kalubalantar zabe na.
“Babu kokwanto wannan hukuncin kotu ya tabbatar da cewa dimukradiyya da kuma bangaren shari’a a kasar na kara samun ci gaba da kuma dorewa.”
Tinubu ya ce duk da barazana da wasu ‘yan siyasa ke yi wa bangaren shari’a musamman kan wannan hukunci, amma ta yi hukunci na adalci.
Ya bukaci sauran ‘yan siyasa da su zo a hada karfi da karfe don gina kasar Najeriya da kawo ci gaba.
Kotun koli ta tabbatar da Tinubu a matsayin shugaban kasa
A wani labarin, kotun koli a Abuja ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya.
Yayin yanke hukuncin, kotun ta yi fatali da korafe-korafen ‘yan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da na LP, Peter Obi.
Asali: Legit.ng