Yanzu Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Tinubu a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Yanzu Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Tinubu a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023

  • A ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, kotun koli ta yi fatali da karar Atiku kan rashin hujjoji
  • Mai shari'a Inyang Okoro ya ce karar da dan takarar shugaban kasar na PDP ya daukaka don kalubalantar zaben shugaban kasa na 2023 bai da inganci
  • Don haka, kotun ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa

Kotun koli ta tabbatar da nasarar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Da take zartar da hukunci a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, kotun ta bayyana cewa karar da Atiku Abubakar, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya shigar bata da inganci, jaridar The Cable ta rahoto.

Koktun koli ta tabbatar da nasarar Tinubu
Yanzu Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Tinubu a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Alkalin kotun, Mai shari'a Inyang Okoro ya ce:

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Koli Ta Yi Watsi da Bukatar Atiku Ta Shigar da Sabbin Hujjoji Kan Tinubu

"A gaba daya batun, ra'ayina shine cewa babu wani cancanta a wannan kara da aka daukaka."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya nemi a soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ta tabbatar da zaben Tinubu a matsayin shugaban kasa.

Fitattun yan Najeriya sun shiga murna

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Bashir Ahmad ya garzaya shafinsa na X wato Twitter don taya yan Najeriya murna kan hukuncin kotun koli da ke tabbatar da nasarar Tinubu.

A cikin wallafa da ya yi jim kadan bayan yanke hukunci, Ahmad ya ce:

"Babu cancanta a cikin karar Atiku Abubakar da Peter Obi, kuma saboda haka anyi watsi da shi. Kotun koli ta tabbatar da nasarar shugaba Bola Tinubu. Ina taya Najeriya murna!"

A nasa bangaren Reno Omokri ya rubuta a shafinsa na X:

"Saboda haka an kori karar da aka daukaka, sannan na tabbatar da cewa Bola Ahmed Tinubu shine zababben shugaban kasar Najeriya."

Kara karanta wannan

Alkalin Alkalai Ariwoola Ya Amince a Haska Hukuncin Kotun Koli Kai Tsaye

Kotu ta yi watsi da bukatar Atiku

A baya mun ji cewa kotun koli a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, ta yi watsi da rokon Atiku Abubakar na gabatar da sabbin shaidu kan shugaban ƙasa Bola Tinubu.

A cewar gidan talabijin na Channels tv, kotun ƙoli ta gaya wa Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP cewa kwanaki 180 da aka ba su damar samun sabbin shaidu sun wuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng