Ganduje ga NNPP: Za Mu Karbe Mulkin Jihar Kano da Aka Yi Mana Fashin Zabe a 2023
- Shugaban jam’iyyar APC ya fitar da jawabi na musamman bayan nasarar da Alhasan Ado Doguwa ya samu a kotun zabe
- Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya taya ‘dan majalisar Doguwa/Tudun Wada murna, ya hango irin haka a shari’ar Gwamnan Kano
- Tun da kotu ta tabbatar da Ado Doguwa ya yi nasara a zaben 2023, Dr. Ganduje ya na ganin Nasiru Gawuna zai karbi mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya sake yin magana game da shari’ar zaben gwamnan jihar Kano.
This Day ta rahoto Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya na cewa magudi aka yi masu zaben bana, yake cewa Kano za ta dawo hannun APC.
Shugaban na jam’iyyar APC ya bayyana cewa za su yi nasara ne a kotun daukaka kara.
Ganduje ya taya Alhassan Doguwa murna
Hakan ya biyo bayan nasarar da Alhassan Ado Doguwa ya samu a kan jam’iyyar NNPP da ‘dan takaranta a kan zaben majalisar tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin da yake jawabi game da nasarar jigon na APC, Abdullahi Ganduje ya kara da cewa gwamnatin NNPP ba ta da farin jini a jihar Kano.
Tsohon Gwamnan yake cewa nasarar da Hon. Alhassan Ado Doguwa ya samu a kotun korafin zabe zai zama silar rikidar siyasar Kano.
A matsayinsa na shugaban APC na kasa baki daya, jaridar ta ce Dr. Ganduje ya taya ‘dan majalisar na Doguwa/Tudunwada murnar nasara.
Jawabin Abdullahi Ganduje
“Kotu ta wanke Alhassan Ado Doguwa a matsayin gwarzon damukaradiyya kuma mai bin doka, wanda ya yarda da shari’a, kwanan nan za mu dare kujerarmu da aka karbe.
Mun jinjinawa kotu da su ka tabbatar da nasarar rinjayen al’umma saboda galabar Doguwa a kotun zabe nasara ce ga damukaradiyya kuma riba ga majalisar tarayya.”
- Dr. Abdullahi Umar Ganduje
A lokacin da Ado Doguwa ya ke shugaban masu rinjaye a majalisa, Ganduje ya ce kowa ya ga irin nasarorin da Femi Gbajabiamilla ya samu.
Abdullahi Umar Ganduje v Abba Kabir Yusuf
A baya aka rahoto tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya cacccaki magajinsa, Abba Kabir Yusuf, ya ce bai kware a mulki ba.
'Dan siyasar ya caccaki Abba kan kalaman da ya yi na sukar rabon tallafin gwamnatin tarayya, daga baya gwamnatinsa ta yi karin haske.
Asali: Legit.ng