Jigon PDP Ya Bukaci Kotun Koli Ta Kori Shugaba Bola Tinubu
- Wani jigo a jam’iyyar PDP, Abdul-Aziz Na’ibi Abubakar, ya bayyana dalilin da ya kamata ya sa kotun ƙoli ta kori shugaban ƙasa Bola Tinubu
- Abubakar ya bukaci kotun ƙolin da ta kori Tinubu, sannan ta bayyana ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar a matsayin shugaban ƙasa
- A cewar Abubakar, kotun ƙoli za ta ceci Najeriya idan ta kori Shugaba Bola Tinubu daga muƙaminsa na shugaban ƙasa
Wani jigo jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Abdul-Aziz Na’ibi Abubakar, ya buƙaci kotun ƙoli ta kori shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce ya kamata kotun ƙoli ta bayyana ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya.
Abubakar, wanda shi ne Darakta Janar na yada labarai na kungiyar Atiku The Light, ya ce korar da kotun koli za ta yi wa Tinubu, za ta ceci Najeriya.
Ya bayyana hakan ne ta shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) @jrnaib2, a ranar Laraba, 25 ga Oktoban 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Domin ceto Najeriya, ya kamata kotun ƙoli ta ayyana Atiku Abubakar a matsayin shugaban ƙasa! #DoleTinubuYaTafi"
Kotun ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci
Kotun ƙoli ta sanya ranar da za ta yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party, suka yi kan nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kotun ƙolin ta sanya ranar da cewa za ta yanke hukuncinta kan ƙararrakin da ƴan takarar suka ɗaukaka, a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoban 2023.
Darektan yaɗa labarai na kotun, Dr. Festus Akande, shi ne ya sanar da ranar da kotun ƙolin za ta yanke hukunci a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Laraba, 25 ga watan Oktoban 2023.
Kotun Koli ta Tanadi Hukunci Kan Karar Atiku, Obi
A wani labarin kuma, kotun ƙoli ta tanadi hukunci kan ƙararrakin da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party suka shigar kan nasarar Shugaba Bola Tinubu.
Ƴan takarar shugaban ƙasar dai ba su gamsu da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke ba, kan nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na ranar, 25 ga watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng