Majalisa Ta Kare Kanta Kan Karbar Motocin Alfarma da Ake Ta Cece-kuce

Majalisa Ta Kare Kanta Kan Karbar Motocin Alfarma da Ake Ta Cece-kuce

  • Yayin da ake ta cece-kuce kan sabbin ministocin majalisun Tarayya, Sunday Karimi ya kare majalisar
  • Karimi, wanda shi ne shugaban kwamitin ayyuka a majalisar, ya ce saboda rashin kyawun hanyoyi ne dole su karbi motocin
  • Ya ce akwai ministoci da ke da motoci na alfarma fiye da uku, amma su kadai ake sakawa ido, me yasa?

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta bayyana dalilin karbar motocin alfarma da ake ta cece-kuce a kai.

Shugaban kwamitin ayyuka a majalisar, Sunday Karimi shi ya bayyana haka yayin hira da manema labarai, Legit ta tattaro.

Majalisa ta kare kanta kan karbar motocin alfarma da ake ta cece-kuce
Majalisa ta yi martani kan karbar motocin alfarma. Hoto: Nigeria Senate.
Asali: UGC

Meye majalisar ke cewa kan karbar motocin alfarma?

Karimi ya bayyana cewa dukkan majalisun biyu sun karbi motocin ne ganin yadda su ke da karfi da juriya wadanda za su kai shekaru hudu.

Kara karanta wannan

Za a Binciki N11.3tr da Buhari da Jonathan su ka kashe a Matatu Daga 2010-2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana haka yayin da ya ke kare matakin nasu na karbar motocin duk da korafe-korafen jama'a, cewar Channels TV.

Ya ce 'yan Najeriya sun saka musu ido yayin ake samun ministoci da ke da suntuma-suntuman motoci fiye da uku a tare da su.

Meye dalilin majalisar na karbar motocin alfarman?

Ya ce:

"Wani minista ya na da 'Land Cruiser' da Prado da sauran motoci amma ba a magana sai mu, me yasa?
"Kuma wadannan motoci da ku ke gani babu karfi, da zarar na je mazaba ta dau daya shikenan, saboda rashin kyan hanyoyi.

Ana cece-kuce kan sabbin ministocin da 'yan majalisar su ka karba wadanda su ka kai Naira miliyan 160 ko wace guda daya.

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke cikin mummunan hali na yanayin tattalin arziki tun bayan cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Bayyana Dalilin Gwangwaje Yan Majalisu da Motocin N160m Duk da Rashin Kudi a Kasa

Amma majalisun Tarayya na wadaka da kudade iya son ransu duk da su ne wakilan al'umma.

'Yan majalisar za su samu suntuma-suntuman motoci

A wani labarin, ana ta cece-kuce bayan wasu motoci da aka bai wa ko wane mamba na majalisar Tarayya.

'Yan Najeriya na ta sukar wannan mataki inda su ke kokawa kan yadda talaka ke cikin kunci.

Sai dai majalisar ta yi martani inda ta ke kare matakin da ta dauka na karbar motocin da cewa su ne maganin rubabbun hanyoyin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.