Majalisar Dattawa Ta Rantsar da Yohanna Madadin Abbo a Matsayin Sanatan Adamawa Ta Arewa

Majalisar Dattawa Ta Rantsar da Yohanna Madadin Abbo a Matsayin Sanatan Adamawa Ta Arewa

  • An rantsar da Amos Yohanna na jam'iyyar PDP a matsayin sabon Sanata a mazabar Adamawa ta Arewa a majalisar Dattawa
  • Yohanna ya maye gurbin Elisha Abbo na jam'iyyar APC bayan kotun daukaka kara ta kwace kujerarshi saboda rashin cika ka'idar cin zabe
  • Rantsarwar ta gudana ne karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar, Jibrin Barau a yau Laraba 25 ga watan Oktoba a Abuja

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta rantsar da Amos Yohanna a matsayin sabon Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa.

Wannan rantsarwar na zuwa ne bayan kotun daukaka kara ta kwace kujerar Sanata Abbo wanda dan jam'iyyar APC ne matsayin zababben Sanata.

Majalisar Dattawa ta rantsar da Yohanna don maye gurbin Abbo a matsayin Sanata
Majalisa Ta Rantsar da Yohanna Madadin Abbo. Hoto: Amos Yohanna, Elisha Abbo.
Asali: Facebook

Yaushe aka rantsar da Yohanna a madadin Sanata Abbo?

Rantsarwar ta gudana ne karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar, Jibrin Barau a dakin majalisar da ke Abuja a yau Laraba 25 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Janar Alkali: Yadda Shari'ar Kisan Gillar Sojan Ke Wakana a Halin Yanzu, An Gabatar da Wadanda Ake Zargi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yohanna daga jam'iyyar PDP ya maye gurbin Abbo bayan kotu ta kwace kujerarshi a makon da ya gabata, Legit ta tattaro.

Punch ta tattaro cewa kotun, yayin yanke hukuncin ta umarci hukumar zabe ta INEC ta bai wa Yohanna satifiket na cin zabe, Vanguard ta tattaro.

Wane martani Abbo ya yi bayan rasa kujerarshi?

Legit Hausa ta tattaro cewa bayan rasa kujerarshi, Abbo ya zargi Godswill Akpabio da shirya masa gadar zare don kwace kujerarshi ta sanata.

Akpabio daga bisani ya barranta kansa da zargin inda ya ce ba shi da hannu a cikin matsalar Abbo dangane da kotun da ta kwace kujerar shi.

Har ila yau, Abbo bayan fahimtar kuskurenshi, ya nemi afuwar Godswill Akpabio inda ya ce ya tabbatar babu hannunsa a ciki kuma ya na neman afuwarshi.

Kara karanta wannan

Za a Binciki N11.3tr da Buhari da Jonathan su ka kashe a Matatu Daga 2010-2023

Abbo ya zargi Akpabio da kutun-kutun don kwace kujerarshi

A wani labarin, Sanatan Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo ya zargi shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da kulle-kulle don ganin ya rasa kujerarshi.

Wannan na zuwa ne bayan kotun daukaka kara ta kwace kujerar tare da mika ta ga Amos Yohanna na jam'iyyar PDP.

Daga bisani sanatan ya ba da hakuri inda ya ce ya fahimci zargin da ya ke yi ba gaskiya ba ne tare da neman afuwarshi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.