Sanata Abbo Ya Nemi Gafarar Akpabio Kan Zargin Hannu a Tsige Shi da Kotu Ta Yi

Sanata Abbo Ya Nemi Gafarar Akpabio Kan Zargin Hannu a Tsige Shi da Kotu Ta Yi

  • Sanata da ke wakiltar Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo ya nemi afuwa a wurin shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio
  • Sanatan ya nemi gafarar ce bayan zargin Akpabio da cewa ya na da hannu a cikin shari'ar kotu da ta kwace kujerarshi a wannan makon
  • Abbo ya nemi afuwar ce yayin hira da gidan talabijin na Arise a yau Laraba 18 ga watan Oktoba

FCT, Abuja - Sanata Elisha Abbo ya nemi gafarar shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Abbo ya zargi Akpabio ne da masa kulle-kulle don ganin ya rasa kujerarsa dalilin kin amincewa da shugabancinsa da su ka yi a baya.

Sanata Abbo ya nemi afuwar Akpabio
A Karshe Sanata Abbo Ya Nemi Gafarar Akpabio. Hoto: Elisha Abbo, Godswill Akpabio.
Asali: Twitter

Meye Sanata Abbo ke zargin Akpabio?

Wannan na zuwa ne bayan kotun daukaka kara ta kwace kujerar Abbo a matsayin sanata da ke wakiltar Adamawa ta Arewa.

Kara karanta wannan

Duniya Ta Yi Tir da Israila a Kan Kashe Fiye da Bayin Allah 500 Kwance a Asibiti

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya nemi afuwar ce a wata hira da gidan talabijin na Arise a yau Laraba 18 ga watan Oktoba.

Ya ce ya tabbatar da cewa babu hannun Akpabio a cikin wannan kulle-kulle amma ya na mai ba shi hakuri akan kuskuren da ya yi a farko.

Meye Sanata Abbo ya ce kan Akpabio?

Ya ce:

"Ni mutum ne mai fadar gaskiya, afuwar da na ke nema shi ne na tabbatar babu hannunsa a cikin wannan lamari.
"Duk wanda ya sanni ya san ni ba na fadar abu don zan samu wani abu, na nemi afuwar ce ba don inason komawa Sanata ba.
"Ganin yadda Akpabio ya yi bayani jiya, da kuma iya abin da mu ke da shi a tare da mu, ba shi da hannu a cikin wannan lamari."

Sanata ya ce ya yi dana sani kuma ya na neman Akpabio ya yafe masa kan zarginshi da ya yi na hannu a cikin abin da ya faru da shi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Rigima Ta Ɓalle a APC, Shugaban Majalisar Dattawa Ya Maida Martani Kan Zargin da Aka Masa

Legit Hausa ta ruwaito cewa kotun daukaka kara da ke zamanta Abuja ta rusa nasarar sanata wanda dan jam'iyyar APC ne.

Kotun daukaka kara ta kwace kujerar Sanata Abbo

A wani labarin, kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta kwace kujerar Sanata Elisha Abbo.

Sanata Abbo na wakiltar mazabar Adamawa ta Arewa a jam'iyyar APC a majalisar Dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.