Da Dumi-Dumi: Kotun Koli Ta Sanar da Ranar Yanke Hukunci a Karar Tinubu v Atiku da Obi
- Zuwa ranar Alhamis Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi za su san makomar takararsu a zaben shugaban kasa
- ‘Yan takaran jam’iyyun na PDP da LP sun tafi babban kotun Najeriya a kan shari’ar zaben 2023 da APC ta samu nasara
- Bola Tinubu zai iya rasa mulki muddin 'yan adawa su ka yi nasara a kotu, idan akasin haka ta faru, dole sai dai su jira 2027
Abuja - Kotun koli ta tsaida gobe a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a kan karar zaben shugaban kasar Najeriya na 2023.
A safiyar yau rahoto ya fito daga Punch cewa kotun koli za ta zauna domin yanke hukuncin karshe a shari’ar zaben shugaban Najeriya.
Atiku Abubakar da ya tsaya takara a jam’iyyar PDP da kuma takwaransa na LP watau Peter Obi su na shari’a da Bola Ahmed Tinubu.
Wace rana kotun koli ta tsaida?
A wata zantawa da aka yi da shi ta wayar salula, Darektan yada labaran kotun kolin ya shaida cewa an sa lokacin yin hukunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Dr. Festus Akande ya fadawa ‘yan jaridar, a ranar Alhamis ne Alkalan babban kotun kasar za su yanke hukunci.
“Gobe, Alhamis, aka tsaida a matsayin ranar hukuncin karar da Atiku Abubakar da Peter Obi su ka daukaka.”
Dr. Festus Akande
Atiku ya nemo hujjoji a CSU
‘Yan takaran jam’iyyar hamayyar su na kalubalantar nasarar da Hukumar INEC ta ba shugaban kasa Bola Tinubu da jam’iyyar APC.
Atiku Abubakar ya kawo sababbin hujjoji daga Amurka da yake so kotun koli ta karba.
...Peter Obi ya yi magana
Da jin kotun koli ta tsaida lokacin da za a sanar da hukunci a karar da aka daukaka, sai aka ji Peter Obi ya fitar da wani jawabi.
‘Dan takaran na jam’iyyar LP ya ce da zarar an yi watsi da dokar kasa, al’umma za su cire rai da tsammanin abin kirki daga kotu.
Jam'iyyarAPC da zaben Bayelsa
Rahoto ya zo cewa ba a taba 'dan takaran kowace jam'iyya a zaben Gwamnan Bayelsa ba illa na APC da tsa tsaida Timipre Sylva.
Hukumar INEC ta ce jam'iyyun AA, ADC, ADP, APGA, APM, APP, BP, LP, NNPP, NRM,PDP, PRP, SDP da ZLP su na da ‘yan takara
Asali: Legit.ng