Zaben Gwamna: INEC Ta Fitar da Sunaye, An Cire ‘Dan Takaran APC a Jihar Bayelsa
- Hukumar INEC ta kasa ta fito da sabon jerin wadanda za a shiga takarar Gwamna da su a zaben jihar Bayelsa
- Babu sunan Timipre Sylva da Joshua Maciver a sanadiyyar kotu da ta haramtawa ‘dan takaran APC shiga zaben
- Rose Oriaran-Anthony ta nuna cewa hukuncin da aka zartar ya jawo aka yi waje da su daga cikin ‘yan takaran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Hukumar zabe mai zaman kan ta watau INEC, ta fitar da sabon jerin sunayen ‘yan takarar gwamna a zaben jihohin Bayelsa da Imo.
Kamar yadda bayanan da aka samu daga shafin hukumar su ka nuna, jam’iyyar APC ba ta da ‘dan takara a zaben gwamna na jihar Bayelsa.
INEC ta yi wa jerin sunayen ‘yan takara kwaskwarima a sakamakon hukuncin da kotu ta zartar na haramtawa Timipre Sylva shiga takara.
Bayelsa: INEC ta cire 'yan takaran APC
A dalilin haka, babu sunan Sylva da abokin takararsa, Joshua Maciver a tikitin na APC duk da tuni shugaban jam'iyyar ya hango nasara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakatariyar hukumar INEC ta kasa, Rose Oriaran-Anthony ta sa hannu a takardar da aka fitar mai dauke da ‘yan takaran kowace jam’iyya.
Duk da an daukaka kara, Oriaran-Anthony ta ce bin umarnin kotu ya jawo aka cire sunayen wasu da su ka yi niyyar shiga takara a zaben.
A ranar 9 ga watan Yuni aka fitar da sunayen ‘yan takara, hukuncin da aka yi da ya shafi takarar APC ya jawo aka fitar da sabuwar sanarwa.
Jam'iyyun da za su yi takara a Bayelsa
Legit ta lura cewa wadanda za su shiga zaben Bayelsa sun hada da jam’iyyar A, AA, ADC, ADP, APGA, APM, APP, BP, LP, NNPP sai kuma NRM.
Ragowar jam’iyyun da za a gwabza da su a Bayelsa sun kunshi: PDP, PRP, SDP da ZLP.
Vanguard ta ce a zaben gwamnan jihar Imo kuwa, an ga sunayen Uchechukwu Ishiodu da Ahumbe Chiazor a matsayin ‘yan takaran PRP.
Sashe na 287 na kundin tsarin mulki ya wajabtawa INEC yin biyayya ga hukuncin kotu.
Rikicin siyasar jihar Zamfara
Ana da labari sabanin siyasar Zamfara ya yi kamari, Dauda Lawal ya fito da bayanai da za su gaskata zargin da yake yi wa Bello Matawalle.
Dauda ya ce rana daya aka zaftare kudin kwangilar filin jirgin daga N28bn zuwa N11bn, kuma aka biya N5.7bn duk da ba ayi komai ba.
Asali: Legit.ng