Gwamnonin Kudu Maso Yamma Sun Ziyarci Gwamna Akeredelu a Ibadan

Gwamnonin Kudu Maso Yamma Sun Ziyarci Gwamna Akeredelu a Ibadan

  • Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, ya karɓi bakuncin gwamnonin Kudu maso Yamma a gidansa da ke Ibadan, jihar Oyo
  • Tun bayan dawowa daga jinya a ƙasar Jamus, gwamnan ya tsaya a gidansa na jihar Oyo ba tare da ya koma jihar Ondo ba
  • Yayin wannan ziyara, gwamnonin sun ce suna ƙara yi wa Akeredolu addu'a kuma suna goyon bayansa ɗari bisa ɗari

Ibadan, jihar Oyo - Gwamnonin Kudu maso Yamma sun kai ziyarar ban girma ga Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, a gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Tun bayan dawowarsa Najeriya daga ƙasar Jamus inda ya tafi neman lafiya, Gwamna Akeredolu, ya ci gaba da zama a gidansa na Ibadan domin ƙara murmure wa.

Gwamnonin Kudu maso Yamma sun ziyarci gwamnan Ondo a Ibadan.
Gwamnonin Kudu Maso Yamma Sun Ziyarci Gwamna Akeredelu a Ibadan Hoto: Leadership
Asali: UGC

Gwamnonin da suka gana da gwamna Akeredelu sun haɗa da Seyi Makinde (Oyo); Babajide Sanwo-Olu (Lagos); Dapo Abiodun (Ogun); da kuma Biodun Oyebanji (Ekiti).

Kara karanta wannan

Manyan Gwamnonin APC 3 Sun Sanya Labule da Gwamnan PDP Dan Tsagin G-5, Bayanai Sun Fito

Tun da farko, Gwamna Makinde ne ya fara karɓan bakuncin tawagar gwamnonin a Ofishinsa da ke Agodi a Ibadan ranar Talata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan wata ganawar sirri da suka yi a ofishin gwamnan Makinde, sai kuma suka zarce zuwa gidan gwamna Akeredolu da ke Jericho a cikin birnin Ibadan.

Gwamnan Ondo ya yaba wa takwarorinsa

Sakataren gwamnan jihar Ondo, Richard Olatunde, ya tabbatar da cewa gwamnonin sun gana da shugabansa a wata sanarwa da ya fitar, rahoton Leadership.

Ya ce Gwamna Akeredolu ya yaba wa gwamnonin bisa nuna masa ana tare kana ya nanata buƙatar ci gaba da haɗa kai tsakanin jihohin Kudu maso Yamma.

Ya kara da cewa "Gwamnonin sun tattauna kan abin da ya shafi kasa da sauran batutuwan da suka shafi yankin da al'ummar Kudu maso Yammacin Najeriya."

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Dalilai 4 da Ka Iya Sanyawa APC Ta Sha Kashi a Jihar Kogi

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce kungiyar gwamnonin Kudu Maso Yamma na yi wa Gwamna Akeredolu addu’a, inda ya ce yana da goyon bayan daukacin gwamnonin yankin.

Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Sahihancin Zaben Gwamnan Adamawa

A wani rahoton mun kawo muku cewa Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa ta sanya ranar yanke hukunci kan nasarar gwamna Ahmadu Fintiri.

'Yar takarar gwamna a inuwar APC, Aishatu Binani, ce ta shigar da ƙarar tana ƙalubalantar sakamakon da INEC ta bayyana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel