Peter Obi Ya Fitar da Sanarwa Bayan Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Karar da Ya Daukaka
- Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya yi magana yayin da ƴan Najeriya ke dakon hukuncin ɗaukaka ƙarar da ya yi kan Shugaba Bola Tinubu
- A wani dogon saƙo da sanya kafafen sada zumunta, Obi ya bayyana matsalar da Najeriya za ta a iya fuskanta idan ɓangaren shari'a bai yi gaskiya ba
- Kalaman Obi na zuwa ne kusan sa'o'i 24 bayan kotun ƙoli mai alƙalai bakwai ta tanadi hukunci kan ƙarar da ya ɗaukaka
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya bayyana cewa al'umma na cikin haɗari idan ana barazana ga doka.
A cikin wani dogon rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba, Obi ya yi nuni da cewa hakan na faruwa ne "lokacin da masu mulki da masu hannu da shuni ke maye gurbin doka."
Omokri Ya Fallasa Katobar Buhari, Ya Fadi Abin da Yan Najeriya Za Su Yi Masa da Sun San Yadda Ya Lalata Kasa
Wane martani Peter Obi ya yi?
Martanin nasa ya zo ne kusan sa'o'i 24 bayan kotun koli ta tanadi hukunci kan ƙarar da ya ɗaukaka kan nasarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obi ya rubuta:
“Idan hakan ta faru, adalci ya zama abin ciniki tsakanin masu mulki da masu hannu da shuni da kuma gurɓatattun ma'aikatan shari'a."
"Lokacin da dimokuradiyya ta ginu bisa rashin adalci, takan buɗe al'umma ga hatsarori masu girma."
Idan ba a manta ba dai a jiya Litinin, 23 ga watan Oktoba, mai shari’a John Okoro, wanda ya jagoranci alƙalan kotun ƙoli su bakwai masu sauraron ɗaukaka ƙarar, ya bayyana cewa za a sanar da ɓangarorin da abin ya shafa da zarar an yanke hukunci.
Obi na son kotun ƙoli ta yi adalci
Obi, lokaci bayan wani lokaci, ya sha kira ga kotun ƙoli da ta yanke hukunci daidai da gaskiyar al'amuran ƴan Najeriya da fatansu a matsayinsu na ƴan kasa masu neman sauyi cikin gaggawa.
Obi ya cigaba da cewa:
"Masu hannu da shuni na iya tattake ƴancin talakawa, domin babu wani hukunci kan keta doka."
"Wannan na iya zama ginshiƙin mayar da dimokuradiyya zuwa mulkin kama karya."
Kotun Koli Ta Dage Sauraron Daukaka Karar Obi, Atiku
A wani labarin kuma, kotun ƙoli ta ɗage cigaba da sauraron ƙarar da Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar kan nasarar Shugaba Tinubu.
Kotun mai alƙalai bakwai ta cimma wannan matsayar ne bayan ta gama sauraron muhawarar lauyoyin ɓangarorin.
Asali: Legit.ng