Zaben Gwamna: Saraki, Adeleke, Da Sauran Jiga-Jigan PDP Sun Isa Kogi Don Kamfen Din Melaye
- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke da sauransu sun isa jihar Kogi gabannin fara kamfen din PDP
- Za a gudanar da zaben gwamnan jihar Kogi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba kuma Sanata Dino Melaye ne dan takarar jam'iyyar
- Saraki ya isa jihar Kogi tare da jiga-jigan babbar jam'iyyar adawa da dama a ranar Talata, 14 ga watan Oktoba
Jihar Kogi - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya isa jihar Kogi, tare da gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke da sauran jiga-jigan jam'iyyar PDP.
Saraki da sauransu sun isa Kogi ne don kaddamar da kamfen din jam'iyyar PDP gabannin zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba.
Dan takarar gwamnan PDP, Sanata Dino Melaye, na cikin yan yan takara uku da suka hada da Ahmed Usman Ododo na APC da Murtala Yakubu-Ajaka na jam'iyyar SDP.
Saraki ya sanar da isarsa jihar ta shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter a baya @bukolasaraki a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yanzun nan na isa jihar Kogi, don kaddamar da kamfen din dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, Sanata Dino Melaye @_dinomelaye”
Mutane da dama sun jikkata yayin da magoya bayan APC da SDP suka kara gabannin zaben gwamnan Kogi
A gefe guda, mun ji a baya cewa an samu hatsaniya a yankin karamar hukumar Idah ta jihar Kogi yayin da magoya bayan jam'iyyar APC da SDP suka yi musayar wuta.
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, mutane da dama sun jikkata a rikicin wanda ya afku a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba.
An tattaro cewa wani jami'in dan sanda da wasu sun ji rauni sakamakon harbi da aka yi sannan an lalata motoci.
Dalilai da ka iya sa APC fadi zaben Kogi
A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto cewa zaɓen gwamnan jihar Kogi na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023. Za a iya cewa shi ne zaɓe mai zuwa da aka fi magana a kansa.
A cewar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), za a fafata zaɓen na gwamnan Kogi tare da na jihohin Imo da Bayelsa.
Asali: Legit.ng