Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Makamaki Ta Kasa ECN

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Makamaki Ta Kasa ECN

  • Bola Ahmed Tinubu ya ɗauko gogaggen injiniya ya naɗa shi a matsayin sabon shugaban hukumar makamashi ta Najeriya (ECN)
  • A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, Tinubu ya naɗa Dokta Abdullahi Mustapha ya jagoranci ECN
  • Shugaban ƙasan ya kuma bayyana cewa yana fatan zai taka rawar a zo a gani a ƙoƙarin gwamnatinsa na gyara ɓangaren samar da makamashi

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Dokta Abdullahi Mustapha, a matsayin sabon shugaban hukumar makamashi ta ƙasa (ECN),

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Mista Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba, 2023.

Bola Tinubu ya naɗa sabon shugaban ECN.
Dokta Abdullahi Mustapha, sabon shugaban hukumar ECN Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro cewa sanarwan na ɗauke da taken, "Shugaban ƙasa Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar ECN."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Wasu Ministoci da Jiga-Jigan FG a Villa, Bayanai Sun Fito

Takaitaccen bayani kan sabon shugaban ECN

Har zuwa wannan naɗi da shugaban ƙasa ya masa, Mustapha ya yi aiki na tsawon sama da shekaru goma a Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga haka kuma yana da kwarewa da gogewa sosai a ɓangarorin Makamashi da Fasahar Sararin Samaniya.

Kwanan nan ne Dokta Mustapha ya kammala digirin digirgir a fannin Injiniya (Mechanical Engeneering), inda ga karanci ɓankaren bunƙasa da sabunta makamashi.

Bai tsaya nan ba, daga nan ya fara gudanar da bincike na bayan kammala digiri na uku a shahararriyar jami'ar nan ta garin Manchester da ke ƙasar Ingila.

Shugaba Tinubu ya ce yana fatan sabon shugaban ECN zai taka rawar gani a yunƙurin gwamnatinsa na samo sabbin hanyoyin samar da makamashin wutar lantarki a Najeriya.

The Cable ta rahoto sanarwan na cewa:

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Fadi Abu 1 da Zai Faru da Jihohin Kasar Nan da Ba a Cire Tallafin Man Fetur Ba

"Muna fatan wannan naɗi zai yi tasiri sosai a ƙoƙarin gwamnati na lalubo hanyoyin samar da wuta tare da haɗin guiwar sauran ɓangarorin gwamnati da nufin bunƙasa harkokin masana'antu."

Ma'aikata Zasu Garƙame NASS da Majalisun Dokoki

A wani rahoton na daban kuma Ma'aikata sun sha alwashin rufe majalisun tarayya da majalisun dokokin jihohi 36 ranar Laraba mai zuwa.

Sun yanke wannan hukuncin ne domin fara yajin aiki kan buƙatarsu.ta ganin na sakarwa majalisu mara su ci gashin kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262