Ana Musayar Yawo Tsakanin Sojoji da PDP Kan Zargin Sace Shugaban Jam’iyyar a Plateau

Ana Musayar Yawo Tsakanin Sojoji da PDP Kan Zargin Sace Shugaban Jam’iyyar a Plateau

  • Rigima na kokarin barkewa tsakanin jam’iyyar PDP da kuma jami’an sojoji a jihar Plateau kan zargin garkuwa da mutane
  • Jam’iyyar na zargin jami’an soji a jihar da sace Mista Ding Tari wanda shi ne shugaban jam’iyyar a Jos ta Kudu
  • Jami’an sojin a martaninsu, sun kalubalanci jam’iyyar da ta kawo hujja na cewa jam’iansu sun sace shugaban jam’iyyar

Jihar Plateau – Jam’iyyar PDP a jihar Plateau na zargin jami’an sojoji da sace shugaban jam’iyyar a Jos ta Kudu, Mista Dung Tari.

Yayin ganawa da amanema labarai a yau Alhamis 19 ga watan Oktoba, shugaban jam’iyyar a jihar, Chris Hassan ya ce wasu jami’an sojoji sun sace Tari da misalin karfe daya na rana bayan kammala ganawarsu, cewar Punch.

PDP na zargin sojoji da sace shugaban jam'iyyar a Plateau
Rikits-rikita yayin da PDP ke zargin sojoji da sace jigon jam'iyyar. Hoto: Plateau State Government.
Asali: Twitter

Meye PDP ke zargin sojoji a Plateau?

Hassan ya ce bayan Tari ya baro dakin taron da su ka gabatar da ganawar a Bukuru da ke Jos ta Kudu, mota kirar Hilux ta jami’an sojoji sun sace shi yayin da ya ke amsa kiran waya.

Kara karanta wannan

Abu Ya Lalace, An Dakatar da Shugaban APC Kan Zargin Yi wa ‘Yar Shekara 14 Ciki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Bayan kammala ganawa da mu ka yi a ofishin jam’iyyar da ke Bukuru, Tari ya dauki dan uwansa a mota don halartar ganawa ta musamman da iyalansu.
“Ya tsaya a gidan mai don amsa kirar waya da aka yi ma sa kwatsam sai ga wata mota kirar Hilux ta tsaya mai lambar jami’an sojoji da kuma kayan sakawansu su ka sace Tari.
“Sannan an dauki dan uwan Tari a wata mota ta daban inda su ka zura da gudu zuwa wani wuri daban.”

Meye martanin sojojin kan zargin PDP a Plateau?

Hassan ya kara da cewa lamarin ya faru ne a ranar 23 ga watan Satumba wanda har zuwa yanzu babu labarin Tari har daga iyalansa da kuma dalilin garkuwa da shi, cewar Ripples.

Amartaninsu, rundunar soji ta bakin kakakin jami’an ma su kokarin kawo zaman lafiya a jihar, Kyaftin Oya James ya karyata wannan labari na garkuwa.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunce Kan Sojojin da Suka Halaka Sheikh Goni Aisami

James ya kalubalanci jam’iyyar ta kawo shaidar cewa jami’an soji ne su ka sace shugaban jam’iyyar a yankin, GistLover ta tattaro.

'Yan bindiga sun hallaka 'yan sa kai 9 a Bauchi

A wani labarin, 'yan bindiga sun yi ajalin wasu 'yan sa kai guda tara a kauyen Gamji da ke karamar hukumar Ningi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kai farmakin ne yayin da 'yan sa kai din ke sintiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.