Babban Jigo a Jam'iyyar PDP a Jihar Kaduna Ya Sauya Sheka Zuwa APC
- Babban jami'in jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ƙasa mai wakiltar jihar Kaduna, ya yi murabus daga muƙaminsa
- Magaji Alhassan ya kuma sanar da sauya sheƙa zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar
- Babban jigon na PDP dai bai bayyana dalilan da suka sanya ya yi murabus tare da ficewa daga jam'iyyar PDP ba
Jihar Kaduna - Wani babban jami'in jam’iyyar PDP na ƙasa mai wakiltar jihar Kaduna, Honorabul Magaji Alhassan ya yi murabus daga muƙaminsa tare da ficewa daga jam'iyyar.
Jaridar Channels tv ta ce ya sanar da murabus ɗinsa ne ta wata wasiƙa da ya aike wa muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, mai ɗauke da kwanan wata na ranar, 5 ga Oktoban 2023.
Hakazalika, Alhassan ya kuma bayyana ficewarsa daga PDP ta wata wasika da ya rubuta wa muƙaddashin shugaban jam'iyyar na gundumar Kwarbai B a ƙaramar hukumar Zariya ta jihar Kaduna, wacce ke ɗauke da kwanan watan ranar, 7 ga watan Oktoban 2023.
Alhassan wanda bai bayyana dalilin sa na ficewa daga jam'iyyar ba, ya miƙa takardar katin zamansa ɗan jam'iyyar da ya aike wa shugaban jam'iyyar na gundumar Kwarbai B.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP na samun koma baya a Kaduna
Jam'iyyar adawan dai ta samu koma baya a jihar Kaduna, inda ƴaƴanta da dama suke ficewa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar.
A ranar 10 ga watan Oktoba, kansiloli 19 da magoya bayansu daga kananan hukumomi 23 da ke jihar Kaduna suka fice daga PDP zuwa APC.
Da suke bayyana ficewarsu daga jam'iyyar PDP a wani taron manema labarai da suka gudanar a babban birnin jihar, sun ce sun koma APC ne saboda irin jagoranci mai ma’ana da gwamnan jihar, Sanata Uba Sani ya ke yi tun bayan da ya ɗare kan mulkin jihar.
Dalilin Ganawar Wike da Saraki
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata majiya mai ƙarfi ta bayyana dalilin sanya labule tsakanin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa.
Majiyar ta bayyana cewa jiga-jigan na jam'iyyar PDP sun gana ne kan batun nemo wanda zai shugabanci jam'iyyar a matakin ƙasa.
Asali: Legit.ng