Daga Karshe, Shugaba Tinubu Ya Nada Bayo Onanuga da Wata Mace a Muƙami

Daga Karshe, Shugaba Tinubu Ya Nada Bayo Onanuga da Wata Mace a Muƙami

  • Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Bayo Onanuga, tsohon mai magana yawun PCC-APC a matsayin mai bada shawara ta musamman
  • Ya kuma naɗa Mis Delu Bulus Yakubu a matsayin babbar mai taimaka masa kan harkokin jin ƙai da yaƙar talauci
  • An yi tunanin ganin sunan Onanuga a cikin tawagar Ministocin shugaban ƙasa amma Tinubu ya yi naɗe-naɗe da dama ba a ga sunansa ba

FCT Abuja - Daga ƙarshe, Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nada Bayo Onanuga a matsayin ba shi shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru.

Daily Trust ta ce Onanuga, tsohon mai magana da yawun kwamitin kamfen shugaban ƙasa na APC, ya yi ƙaurin suna wajen kokarin kare shugaba Tinubu.

Shugaba ya nada Bayo Onanuga a mukami.
Daga Karshe, Shugaba Tinubu Ya Nada Bayo Onanuga da Wata Mace a Muƙami Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Bayo Onanuga
Asali: UGC

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Chief Ajuri Ngelale, shi ne ya bayyana wannan naɗin na Onanuga a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a da daddare.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Yayin da Tsohon Minista Kuma Babban Jigon APC Ya Rasu a Arewa

Bayan Onanuga, shugaban ƙasar ya kuma naɗa Ms. Delu Bulus Yakubu a matsayin mai taimaka masa ta musamman kan harkokin jin ƙai da yaye taauci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wannan naɗe-naɗe wani ɓangare ne na ƙara ingancin aiki da yauƙaƙa dangantaka tsakanin fadar shugaban ƙasa da wasu ma'aikatun tarayya, rahoton Channels tv.

Sabbin naɗe-naɗen da Tinubu ya yi

"A wani ɓangaren ƙara inganta aiki da alaƙa tsakanin fadar shugaban ƙasa da ma'aikatu, Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗa wasu kwararru kan tsari da harkokin ma'aikataun tarayya."
"Mista Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru. Ms. Delu Bulus Yakubu a matsayin babbar mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin jin ƙai da yaye talauci."
"Shugaban ƙasa ya yi fatan alheri ga sabbin hadiman da aka naɗa domin su gudanar da ayyukan da aka ɗora musu."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: A Karo Na Biyu, Shugaba Tinubu Ya Naɗa Ɗalibar Jami'ar Arewa a Babban Muƙami

- Chief Ajuri Ngelale.

Duba da rawar da ya taka a yakin neman zabe, wasu sun yi tunanin za a nada Onanuga a matsayin minista, amma Tinubu ya yi nade-nade da dama ba tare da sanya sunansa ba.

Duk da haka bai yi ƙasa a guiwa ba wajen kare shugaban ƙasa, wanda na baya-bayan nan an ji Onanuna yana tare wa Tinubu faɗa kan takardar karatun jami'ar jihar Chicago.

Jerin Sunayen Mutane 14 Da Tinubu Ya Bai Wa Sabbin Mukamai

A wani rahoton na daban kuma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake yin wasu sabbin nade-nade guda 14 a gwamnatinsa.

Kakakin shugaban kasar ne sanar da sabbin nade-naden a cikin wata sanarwa da ta saki a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262