Peter Obi Ya Ce Tinubu Ya Jawo Wa Najeriya Abin Kunya a Idon Duniya Kan Takardun Bogi
- Peter Obi, dan takarar jam’iyyar Labour ya bayyana yadda Bola Tinubu ya rusa martabar Najeriya a idon duniya
- Obi ya bayyana haka a yau Laraba 11 ga watan Oktoba a Abuja yayin ganawa da manema labarai
- Ya ce matsalar takardun Tinubu abin takaici ne wanda ya jawo wa Najeriya abin kunya a idon kasashen duniya
FCT, Abuja – Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya nuna damuwarshi kan yadda Tinubu ya rusa martabar Najeriya a idon duniya.
Obi na Magana ne kan dambarwar takardun Bola Tinubu da ke jawo cece-kuce wanda hakan zubar da mutuncin kasar ya yi, Legit ta tattaro.
Meye Peter Obi ke cewa kan Tinubu?
Dan takarar shugaban ya bayyana haka ne a yau Laraba 11 ga watan Oktoba yayin ganawa da manema labarai a Abuja.
Cikakken Jerin Takardun Karatun da Tinubu, Atiku, Peter Obi, Kwankwaso Suka Ba INEC Kafin Zaben 2023
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce almundahana da Tinubu ya yi a takardunsa na Jami’ar Chicago shi ne ya zubar wa Najeriya mutunci a idon duniya.
Obi ya ce:
“Matsalar Jami’ar Chicago, da kuma korafe-korafe da su ka biyo bayan takardun Tinubu ya kara zubar wa Najeriya mutunci a idon duniya.”
Arise TV ta wallafa faifan bidiyon Peter Obi a shafin Twitter:
Meye Atiku ke cewa kan Tinubu?
Takwarshi na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya zargi Shugaba Bola Tinubu kan mika takardun bogi ga Hukumar Zabe mai Zaman Kanta, INEC.
Atiku ya bukaci kotun majistare a Amurka ta umarci Jami’ar Chicago da ta sake takardun Tinubu a gare shi.
Daga bisani dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya samu abin da ya ke nema bayan Jami’ar ta saki takardun gare shi.
Yayin da Atiku a ganawarshi da ‘yan jaridu a ranar Alhamis 5 ga watan Oktoba a Abuja ya zargi cewa takardar Tinubu na dauke da sunan wata bakar fata ‘yar Amurka.
Kotun Koli: Wata Sabuwa Yayin da Shararren Malami Ya Yi Hasashen Sabon Zabe Tsakanin Atiku Da Peter Obi
Atiku daga bisani ya yi amfani da wannan hujjar wurin hada wa da sauran don kalubalantar Tinubu a kotun koli.
Peter Obi ya daukaka kara don kalubalantar Tinubu
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya daukaka kara don kalubalantar hukuncin kotun kararrakin zabe.
Obi ya ya bayyana cewa a hukuncin kotun akwai kura-kurai da dama wanda su ka yi fatali da hujjojinsa.
Asali: Legit.ng