“Za Ku Gani Zai Zo Ya Wuce”: Malami Ya Ce Za a Sake Zabe Tsakanin Atiku Da Obi
- A kokarinsa na ganin an tsige Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daga karagar mulki, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya garzaya kotun koli
- Haka kuma, tsohon na hannun damar Obi, Atiku Abubakar na PDP shima ya bi sahu kuma ya nemi gabatar da sabon hujja kan Tinubu a kotun koli
- Da yake magana kan dambarwar siyasar Najeriya, wani fasto, Kingsley Okwuwe,ya yi hasashen sake zabe tsakanin Atiku da Obi
FCT, Abuja - Fasto Kingsley Okwuwe na cocin Revival and Restoration Global Mission ya yi hasashen sake zabe tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi.
Fasto Okwuwe ya yi hasashen ne a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba, ta shafinsa na YouTube.
Fasto ya yi hasashen makomar siyasar Najeriya
A cewarsa, Shugaban kasa Tinubu zai bar kujerar shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Za a tilastawa BAT (yana magana ne a kan Tinubu) barin kujerar shugaban kasa kuma za a sake zabe tsakanin Atiku da Peter Obi.
“Za ku gani wannan zai zo ya wuce. Allah ya sa hannu kan lamarin kasar nan. Allah na so ya mayar da Najeriya zuwa sabuwar Najeriya.
“Wadanda ke kusa da BAT su sanar da shi abun da Ubangiji ke fadi.
“Na rigada na fada maku wani hasashe inda wasu bangarorin adawa biyu suka mamaye shi (Tinubu), sannan ya kai kasa. Ku tuna na kuma fada maku cewa fada zai kaure tsakanin wasu manyan giwa biyu; na fada maku cewa daya daga cikinsu zai fito daga ainahin jam’iyyar. Wadannan giwaye biyu sun rigada sun fara fada. Kuma daga abun da nake hangowa, zai zama fada mai zafi. Na yi wannan hasashen tun a watan Yuni.
“Abun da zai faru nufi ne na Allah. Za a sake zaben kuma za a cimma mafi alkhairi.”
Jami'ar CSU: Babu hujja cewa Tinubu ya kirkiri takardan jabu, In Ji BBC
A wani labarin, mun ji cewa tawagar tantance bayanai na gaskiya na Kafar Watsa Labarai na Birtaniya (BBC) ta wallafa rahoto kan batun takardan shaidar karatun Shugaba Bola Tinubu na Najeriya.
Wadanda suka rubuta rahoton mai taken: 'Bola Tinubu diploma: No evidence Nigeria’s president forged college record’ sun cimma matsayar cewa Shugaba Tinubu bai kirkiri takardan karatu na bogi ba.
Asali: Legit.ng