Kansilolin PDP 19 a Jihar Kaduna Sun Sauya Sheka Zuwa APC
- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Kaduna ta samu ƙarin yawan mamboɓi
- Kansiloli 19 na jam'iyyar PDP da magoya bayansi daga ƙananan hukumomi 23 sun koma jam'iyyar APC
- Kansilolin sun bayyana cewa gamsuwa da salon mulkin gwamna Uɓa Sani ne ya sanya suka sauya sheƙa zuwa APC
Jihar Kaduna - Kansiloli 19 na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna tare da magoya bayansu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki, cewar rahoton Channels tv.
Da suke bayyana ficewarsu daga jam'iyyar PDP a wani taron manema labarai a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, sun ce sun koma APC ne saboda irin jagoranci mai ma’ana da gwamnan jihar, Sanata Uba Sani, yake yin tun bayan hawansa mulki.
Kansila mai wakiltar gundumar Yelwa a ƙaramar hukumar Chikun, Ishaku Duchi, shi ne wanda ya jagoranci sauran wadanda suka sauya sheƙa zuwa ofishin yaƙin neman zaɓe na jam’iyyar APC.
Sun shawarci ɗan takarar gwamnan PDP
Ishaku ya kuma roki ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Isah Ashiru, da ya janye ƙararsa da ya shigar yana ƙalubalantar zaben gwamna Uba Sani a kotun daukaka kara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma buƙaci da a maimakon ƙarae ya zo su yi aiki tare wajen ciyar da jihar gaba.
Wasu kuma daga kansilolin sun yi iƙirarin cewa sun ɓata lokaci mai amfani a jam'iyyar adawa ba tare da samun wata riba ba, kafin su yanke shawarar komawa jam’iyyar APC saboda nagartaccen shugabanci na gwamna Uba Sani.
Wane irin yabo APC ta yi musu?
Yayin da yake karbar waɗanda suka sauya shekar, sakataren tsare-tsare na APC na jihar Kaduna, Kawu Yakasai, ya yaba musu bisa yadda suka samu ƙwarin gwiwar dawowa jam'iyyar APC.
Ya kuma ba da tabbacin cewa babu wanda za a bari a baya a wajen harkokin tafiyar da jihar Kaduna a ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Gwamnan PDP Ya Ba Abokin Hamayyarsa Mukami
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Delta na jam'iyyar PDP ya ba wanda ya yi takarar gwamna da shi a jam'iyyar YPP muƙami mai gwaɓi a gwamnatinsa.
Gwamna Sheriff Oborevwori ya naɗa Sunny Ofehe a matsayin mai taimaka masa kan harkokin waje.
Asali: Legit.ng