Jam'iyyar Labour Party Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Peter Obi Ba Zai Yi Aiki Da Gwamnatin Tinubu Ba

Jam'iyyar Labour Party Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Peter Obi Ba Zai Yi Aiki Da Gwamnatin Tinubu Ba

  • Jam'iyyar Labour Party (LP) ta ce hankalin Peter Obi yana kan ƙwato nasararsa da aka ƙwace a kotun ƙoli
  • Shugabannin jam’iyyar sun ce babu yadda za ayi Obi ya yi aiki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Mai ba jam'iyyar LP shawara kan harkokin shari'a, Kehinde Edun, ya ce Obi ba zai yi aiki da "wani wanda zamansa babu tabbas a ofishin ba".

FCT, Abuja - Jam’iyyar Labour (LP) ta bayyana dalilin da ya sa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, ba zai iya aiki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba.

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa, Obiora Ifoh da mai ba LP shawara kan harkokin shari’a na ƙasa, Kehinde Edun, a cikin wata tattaunawa daban-daban da jaridar The Punch, sun ce Obi ba zai iya yin aiki da gwamnatin Tinubu ba domin haɗin kan ƙasa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Nade 5 Masu Muhimmanci

Peter Obi ba zai yi aiki a gwamnatin Tinubu ba
Jam'iyyar Labour Party ta ce Obi ba zai iya a gwamnatin Tinubu ba Hoto: Mr Peter Obi/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugabannin sun bayyana haka ne a lokacin da suke mayar da martani kan hasashen cewa Obi zai fi son yin aiki da Shugaba Tinubu fiye da ɗan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, saboda ƙin amincewa da kiran da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi masa na su yi aiki tare.

LP ta ce Obi ya lashe zaɓen 2023

Mai ba jam'iyyar LP shawara kan harkokin shari’a ya ce tuni Obi da jam'iyyar suka bayyana matsayarsu cewa tsohon gwamnan na jihar Anambra shi ne ya lashe zaɓen 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Edun ya ce jam'iyyar Labour tana bin kadin nasarar Obi a kotun ƙoli kuma ba ta da shirin yin aiki da gwamnatin Tinubu.

A kalamansa:

"Wannan shine dalilin da ya sa ba dai ayi maganar Obi ba, wanda shi ne ya lashe zaɓe, ya je yana aiki a ƙarƙashin wanda ofishin ba na sa bane. Idan har ba ƙarshen wannan ƙarar mu ka gani a kotun ƙoli ba, ba a gama wasan ba."

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki a Jihar Arewa, Sun Yi Awon Gaba Da Manoma Masu Yawa

Hakazalika mai magana da yawun LP ya ce ba za a ɗauke wa Peter Obi hankali ba dangane da nasararsa da yake son ƙwatowa a kotun ƙoli.

Ifoh ya bayyana cewa:

"Har yanzu muna kan ƙwato nasararmu da aka sace ta hanyar ɗaukaka ƙarar da muka shigar a kotun ƙoli. Babu yadda za ayi a ga ɗan takararmu yana yi wa wannan gwamnatin aiki. A yanzu ya mayar da hankali ne kan ɗaukaka ƙara a kotun ƙoli."

Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Nade

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗe a gwamnatinsa.

Shugaban ƙasar ya naɗa sabbin mataimaka na musamman har mutum biyar da za su yi aiki a ƙarƙashin ofishin yaɗa labarai na shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng