Minista Ya Yi Hasashen Yadda Shari’ar Tinubu v Atiku Za Ta Kare a Kotun Koli
- Festus Keyamo SAN ya fadawa magoya bayan Atiku Abubakar su bar murnar an samu Bola Tinubu da laifi
- Ministan harkokin jiragen saman ya ce PDP na bukatar jami’ar CSU ta nesanta kan ta daga takardun Tinubu
- Zabin da ya ragewa lauyoyin Atiku shi ne su nemo wadanda su ka shugaban kasa satifiket a madadin CSU
Abuja - Festus Keyamo ya maida martani ga magoya bayan Atiku Abubakar da masu sa ran kotu ta tunbuke Bola Ahmed Tinubu.
A ranar Lahadi, 8 ga watan Oktoba 2023, Festus Keyamo SAN ya maida martani ga masu zargin shugaban kasa da karyar takardu.
Lauyan ya yi kaca-kaca da duk masu wannan magana a shafin Twitter, ya ce tun asali ba su cancanci ya maida raddi gare su ba.
Keyamo ya yi shekaru 30 ya na shiga kotu
Keyamo ya ke cewa ya shafe sama da shekaru 30 a matsayin lauya mai tuhuma ko mai bada kariya, don haka ya dace ya yi magana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanin ministan ya ce dauko tsohuwar maganar da ya taba yi a game da shari’ar Muhammadu Buhari ba za ta iya zama hujja ba.
Tinubu: Aikin da yake gaban Lauyoyin Atiku
Kafin lauyoyin Atiku Abubakar su gamsar da kotu cewa an samu Bola Tinubu da zargin badakalar takardar shaida, sai an bi matakai.
Hakkin lauyoyi masu kara ne su nuna inda jami’ar CSU ta nesanta kan ta daga satifiket din da Bola Tinubu ya gabatar wajen zabe.
Idan ba haka ba, dole sai an kafa hujja da wanda ya mallakawa Tinubu takardarsa.
"Ba za ka iya zargi ko tabbatar da karyar takarda ba har sai wadanda su ka bada takardar sun yi da’awar rashin ingancinta ko kuwa akwai hujjar yankan shakku na bincike da aka yi da karara ya tabbatar da an taba takardar ko kuwa kirkirarsa aka yi (a fuskar doka)
Saboda haka a shari’ar Atiku Abubakar da jami’ar Chicago, muddin jami’ar ba ta fito dili ta ce ba ta canza takardun karatu ba, sai dai ‘yan kasuwa su bada a madadinta, to surutu a kan batun bata lokaci ne har sai an samu wanda ya bada takardar shaida ga Bola Tinubu ya tabbatar da rashin ingancinsa.
- Festus Keyamo SAN
A cewar Keyamo, aikin Atiku Abubakar ne ya shiga neman wanda ya ba Tinubu takardar shaidar, sai ya kafa hujja da shi a gaban kotun koli.
Sanatoci sun goyi bayan Tinubu
A badakalar takardun karatu, ku na da labari tsofaffin ‘Yan majalisa da-dama ba su goyon bayan Atiku Abubakar a shari’ar da yake yi.
Sanata Basheer Lado ya ce su na sane da zargi maras tushe da yake kewaye da Shugaban kasa, ya na mai rokon kotun koli ta yi adalci.
Asali: Legit.ng