Jigon NNPP Aniebonam Ya Ce Jam'iyyar Ba Za Ta Rasa Mulkin Kano Ba

Jigon NNPP Aniebonam Ya Ce Jam'iyyar Ba Za Ta Rasa Mulkin Kano Ba

  • Wanda ya kafa jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya yi magana kan ƙarar da jam'iyyar ta ɗaukaka kan hukuncin zaɓen gwamnan Kano
  • Boniface Aniebonam ya yi nuni da cewa jam'iyyar ba za ta rasa mulkin Kano ba domin kotun za ta yi adalci
  • Jigon na NNPP ya ƙara da cewa kamar yadda Gawuna ya taya Abba murna bayan zaɓe, hakan za ta ƙara kasancewa bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara

Ikeja, Legas - Dr. Boniface Aniebonam wanda ya kafa jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) mai kayan marmari, ya ce kujerar gwamnan jihar Kano ba za ta suɓuce a hannun jam'iyyar ba.

Jaridar Vanguard ta ce Aniebonam ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 8 ga watan Oktoba a Legas.

Jigon NNPP ya ce NNPP ba za ta rasa Kano ba
Jigon NNPP ya ce Abba ba zai rasa mulkin Kano ba Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

A ranar 20 ga watan Satumba ne dai kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano, mai alƙalai uku ta soke nasarar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris 2023.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Da Wasu Manyan Shugabannin Mata Sun Ƙara Ruguza Jam'iyyar PDP a Arewa

Kotun ta bayyana ɗan takarar jam'iyyar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin sahihin wanda wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa NNPP ba za ta rasa Kano ba?

Wanda ya kafa NNPP ya yi nuni da cewa da ikon Allah, jam'iyyar ba za ta yi rashin nasara ba a kotun ɗaukaka ƙara ko a kotun koli ba.

A kalamansa:

"Ko shakka babu abin da NNPP a matsayinta na jam'iyyar siyasa da ɗan takararta suka samu a kotun sauraron ƙararrakin zabe ta jihar Kano, hukuncin mutum ne ba na Allah ba."
"Wanda yake tare da Allah yana tare da komai, saboda haka mu cigaba da zaman lafiya muna jiran abin da Allah zai yi a kotun ɗaukaka ƙara da kotun ƙoli."

Aniebonam ya ce tuni ɗan takarar gwamnan APC ya taya Yusuf murna jim kaɗan bayan bayyana sakamakon zaben kuma bai je ya ƙalubalanci sakamakon a kotun ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Babban Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa Tsagin Adawa

Ya ƙara da cewa, hakan zai kasance a kotun ɗaukaka ƙara inda za a yi wa NNPP adalci da yardar Allah.

Abba Ya Kai Ziyarar Bazata a Asibiti

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar bazata cikin dare a wani asibiti domin duba yadda abubuwa suke tafiya.

Gwamnan a yayin ziyarar da ya kai ya rabawa majinyata N20,000 kowannensu domin sauƙaƙe musu halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng