Sanatoci 107 Sun Tsoma Baki a Lamarin Tinubu v Atiku, Sun Goyi Bayan Shugaban Kasa

Sanatoci 107 Sun Tsoma Baki a Lamarin Tinubu v Atiku, Sun Goyi Bayan Shugaban Kasa

  • Wasu tsofaffin ‘Yan majalisar tarayya su na neman kotu ta wanke Bola Tinubu daga zargin 'yan adawa
  • Atiku Abubakar ya na tuhumar Shugaban kasa da badakalar takardun karatun jami'a a kasar waje
  • ‘Yan siyasar sun ce ya kamata ayi hattara wajen raba gardamar da ake yi tun zaben shugaban kasa

Abuja - Ganin yadda ake ta surutu a kan zargin Bola Tinubu da yin karyar takardun karatu, tsofaffin ‘yan majalisa sun yi magana.

A jiya ne Vanguard ta rahoto cewa Sanatoci 107 da su ka bar ofis sun nuna bukatar a bi tsarin mulki a wajen warware tirka-tirkar.

‘Yan majalisar da su ka nuna su na goyon bayan shugaban da ke kotu, sun ce dole ne sai an yi taka-tsan-tsan da zargin badakalar.

Kara karanta wannan

Minista Ya Yi Hasashen Yadda Shari’ar Tinubu v Atiku Za Ta Kare a Kotun Koli

Bola Tinubu
Atiku ya taso Bola Tinubu a gaba Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Sanata Basheer Lado su na tare da Tinubu

Leadership ta ce Shugaban Sanatocin da ke da ra’ayin nan, Basheer Lado a jawabinsa, ya ce su na ankare da halin da ake ciki a halin yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mu na sane da zargi mara tushe da ke kewaye da takardun shugaban kasa Tinubu, wanda hakan ya jawo surutu a bainar jama’a.
Mun yi imani akwai bukatar a jaddada sai an yi hattara tare da bin doka da tsarin mulki.
Shugaba Tinubu ya kasance jajirtaccen shugaba da yake yi wa kasarmu hidima da kyau kuma cikin daraja na tsawon shekara da shekaru.

- Basheer Lado

Kotu za ta kori karar Atiku?

Atiku Abubakar ya na tuhumar Bola Tinubu da amfani da takardar kammala jami’a ta bogi, zargin da shugaban kasar ya musanya.

Sanata Lado ya ce su na fatan kotu za ta yi adalci a kan tuhumar da ‘yan adawa a karkashin jagorancin Atiku Abubakar su ke yi.

Kara karanta wannan

Yanzu aka fara: Sanata ya ce mulkin Tinubu ya dace da Najeriya, ya fadi dalilai

Akwai aiki gaban Atiku - Festus Keyamo

Da ya ke magana a dandalin Twitter, Festus Keyamo ya ce Atiku ba zai iya sa kotun koli ta tsige Mai girma shugaban Najeriya ba.

A matsayinsa na kwararren lauya na shekara da shekaru, Festus Keyamo SAN ya ce akwai karin hujjojin da Atiku ya ke bukata a kotu.

Ministan yake cewa wajibi ne sai lauyoyin ‘dan takaran PDP sun gabatar da wadanda ake ikirarin sun buga takardar shaidar Tinubu.

Ra'ayin Dalung a kan Tinubu

Shi kuwa Salomon Dalung cewa ya yi har yanzu ‘Yan Najeriya ba su farfado daga cire tallafin fetur da Bola Tinubu ya yi a Mayu ba.

Da yake bayani a kan gwamnati mai-ci, Dalung ya ce barin darajar Naira a hannun kasuwa tamkar tura soja yaki ne babu bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng