Atiku Ya Shigar Da Sabbin Shaidu Kan Shugaba Tinubu a Kotun Koli
- A wani gagarumin sauyi a fagen siyasar Najeriya, dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya shigar da sabbin shaidu a gaban kotun koli
- Atiku ya zargi shugaban ƙasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu da laifin ƙarya da amfani da takardun bogi
- Wannan sabuwar shaidar da Atiku ya gabatar, ta samo asali ne daga bayanan takardun karatun Tinubu wanda ya samu daga jami'ar jihar Chicago
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya shigar da sabuwar ‘shaida' ta yin amfani da takardun jabu a kan Shugaba Bola Tinubu.
Rahoton jaridar Vanguard na ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba, ya ce sabuwar ‘shaidar’ ta fito ne daga birnin Chicago na ƙasar Amurka.
Sabuwar ‘shaidar’ Atiku akan Tinubu
Ana sa ran tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku, zai gabatar da sabbin shaidun a gaban kotun ƙoli waɗanda ke nuna rashin cancantar Shugaba Tinubu a zaɓen watan Fabrairun 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar wata sanarwa a ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba, Phrank Shaibu, mai taimaka wa ɗan takarar PDP a fannin sadarwa, Atiku ya yi iƙirarin cewa takardar shaidar satifiket na jami'ar jihar Chicago (CSU) da Tinubu ya yi amfani da ita ya miƙa wa hukumar INEC kafin zaɓen 2023, ta ƙarya ce.
Ya haƙiƙance cewa takardar shaidar kammala kararun diflomar ta jabu ce.
A cikin wata takarda da tawagar lauyoyin sa karkashin jagorancin Chris Uche, (SAN) ya shigar, Atiku ya buƙaci kotun koli da ta yi amfani da umarni na 2 na doka ta 12 ta shekarar 1985 domin karɓar sabbin shaidun takardar jabu kan ɗaukaka ƙarar da ya shigar a gaban kotun.
Waɗanda aka shigar a ƙarar sun haɗa da INEC, Tinubu, da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a matsayi na ɗaya zuwa na uku.
A halin da ake ciki, har yanzu ba a sanya ranar sauraron karar ba.
Tinubu Ya Yi Ganganci, Kperogi
A wani labarin kuma, Farfesa Farooq Kperogi ya yi magana kan dambarwar shaidar kammala karatun Shugaba Tinubu da ake yi.
Farfesan ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi ganganci wajen miƙa takardar shaidar kammala karatu ga hukumar INEC, waɗanda ba daga jami'ar CSU suka fito ba.
Asali: Legit.ng