INEC Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Musanta Zare Hannu a Daukaka Kara Kan Zaben Gwamnan Kano

INEC Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Musanta Zare Hannu a Daukaka Kara Kan Zaben Gwamnan Kano

  • Hukuma INEC ta yi amai ta lashe akan daukaka kara kan hukuncin kotun zaben gwamnan jihar Kano
  • Hukumar zabe ta ce bata tsame hannu daga shari'ar zaben gwamnan Kano da aka daukaka kara ba
  • Kwamishinan INEC, Sam Olumekun ya jaddada cewar manufarsu kan batu irin na shari'ar zaben Kano, ba ta canza ba

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sake daukaka kararta kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke.

Hakan na zuwa ne yan awanni bayan hukumar zaben, a cikin wata wasika da ta aike daga hedkwatarta, ta sanar da muradinta na janye karar.

INEC ta ce bata janye daukaka kara a zaben gwamnan Kano ba
INEC Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Musanta Zare Hannu a Daukaka Kara Kan Zaben Gwamnan Kano Hoto: Olukayode Jaiyeola
Asali: Getty Images

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Suleiman Alkali, shugaban sashin shari'a na ofishin INEC a Kano, a cikin wata wasika zuwa ga sakataren kotun zaben gwamnan Kano, a madadin kwamishinan zabe ya ce:

Kara karanta wannan

Cikakkun Sunaye: Jerin Jihohin Da PDP, APC da Labour Party Suka Yi Nasara a Kotun Zabe

"Hedikwatar hukumar INEC ta umurce ni da cewa a hukumance ba ta da wani dalili na daukaka kara kan wannan hukunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Saboda haka, sashen hukumar da ke kula da harkokin shari'a da kuma kwamishinan hukumar na kasa mai kula da shiyyar Kano sun ba da umarnin a janye karar, kuma a mika duk wani tsari na duk daukaka kara ga ofishin Kano."

INEC ta musanta zare hannu a daukaka kara game da zaben gwamnan Kano

Daily Nigerian ta rahoto cewa sabbin rahotanni sun tabbatar da cewar hukumar zaben za ta ci gaba da daukaka kararta kan APC da hukuncin kotun zaben gwamnan a kotun daukaka kara.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da ilmantar da masu zabe na INEC, Sam Olumekun ya fitar a ranar Lahadi, 7 ga watan Oktoba, hukumar ta ce manufarta kan batu irin na shari'ar zaben Kano, ba ta canza ba.

Kara karanta wannan

Kano: Dan Majalisar Da Ya Rasa Kujerarsa Ya Yi Nasara a Kotun Daukaka Kara

INEC ta ce an ja hankalinta zuwa ga wata sanarwa da jami’inta na sashen shari’a a ofishinta da ke Kano ya fitar wanda ke nuni da cewa hukumar ta janye karar zaben gwamnan Kano da ta yi.

Sanarwar ta ce:

"An ja hankalin hukumar zuwa wasu rahotannin midiya game da wata wasika da ofishin shari'armu ta Kano ta fitar wanda ke nuna cewa hukumar ta janye daukaka kara a shari'ar zaben gwamnan Kano da ke gudana.
"Muna so mu bayyana cewa ba a amince da wannan wasikar ba. Kuma tuni muka janye sanarwar, kuma an tsawatar wa jami’in.
"Saboda haka ana shawartan jama'a da su yi watsi da rade-radin cewa hukumar ta janye daga shari'ar ko ma abu mafi muni cewa ta yi watsi da daukaka karar."

Rudani a APC, ‘yan jam’iyya sun tona wadanda su ka goyi bayan Atiku a 2023

A wani labarin, shugabannin jam’iyyar APC na neman tado tsohon rikicinsu a sakamakon ziyarar da su ka kai wa Abdullahi Umar Ganduje.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa bangarorin APC na reshen jihar Ribas sun ziyarci shugaban jam’iyya na kasa a sakatariya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng