Kperogi Ya Ce Tinubu Bai Saba Doka Ba Kan Dambarwar Satifiket, Ya Bayyana Dalilai
- Farfesa Farooq Kperogi ya sake martani kan matsalar takardun karatun Shugaba Tinubu da ke ta da jijiyoyin wuya
- Kperogi ya ce babu inda Tinubu ya saba doka saboda a Amurka satifiket ba shi da wani tasiri wurin kammala karatu
- Wannan martani na shi ya sha bam-ban na wanda ya fitar a kwanaki inda ya ke zargin Tinubu da saba doka
Chicago, Amurka – Farooq Kperogi wani mai fashin baki da ke zama a Amurka ya ce Shugaba Tinubu bai aikata wani laifi ba dangane da takardun karatunshi.
Kperogi wanda asali dan Najeriya ne ya ce Tinubu ba shi da laifi tun da Jami’ar ta tabbatar da takardunsa, Legit ta tattaro.
Meye Kperogi ya ce kan satifiket na Tinubu?
Farooq ya bayyana haka ne a yau Asabar 7 ga watan Oktoba inda ya ce Satifiket a Amurka ba shi da wani amfani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce magatakardar Jami’ar ya tabbatar da sahihancin takardun Tinubu inda ya bayyana sakamonsa da kuma tsohon dan ajinsu.
Ya ce:
“Ba a amfani da satifiket a ma’aunin kammala makaranta a Amurka don haka babu yadda za a yi badakala da shi ta inda ya dace.
“Kwafin sakamakon ne kawai ake amfani da shi wurin tabbatar da kammala karatu da kuma sakandare.”
Wane karin haske Kperogi ya yi kan satifiket na Tinubu?
Ya kara da cewa:
“Inda ace Tinubu ya tura sakamakon da ke da matsala da shi ne zai zama takardun bogi wanda za a iya cewa ya aikata laifi.”
Wannan martani na Kperogi ya sabawa maganarsa ta farko inda ya ce satifiket da Tinubu ya mika hukumar Zabe ta INEC ya saba da na Jami’ar wanda ya zarge shi da mallakar takardun bogi."
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar shi ya bi diddigi har aka tono batun takardun Tinubu.
Atiku ya nemi hadin kan Peter Obi, Kwankwaso kan takardun Tinubu
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nemi goyon bayan 'yan takarar shugaban kasa kan shari'ar zabe.
Atiku ya roki Kwankwaso da Peter Obi don hada kai da tabbatar da gaskiyar takardun Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng