APC Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotu Na Tabbatar Da Nasarar Gwamna Alex Otti Na Abia

APC Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotu Na Tabbatar Da Nasarar Gwamna Alex Otti Na Abia

  • Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta mayar da martani kan hukuncin da ya tabbatar da zaben gwamna Alex Otti na jam’iyyar Labour Party (LP) a jihar Abia
  • Shugaban jam'iyyar APC a jihar, Dr. Kingsley Ononogbu ya yi watsi da hukuncin kotun, yana mai bayyana hukuncin a matsayin rashin adalci
  • Ononogbu ya bayyana cewa jam'iyyar ta umarci tawagar lauyoyin ta da su daukaka ƙara kan hukuncin kotun da ya tabbatar da zaben ranar 18 ga Maris

Umuahia, jihar Abia - Jam’iyyar APC reshen jihar Abia ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar ta yanke na tabbatar da nasarar Gwamna Alex Otti na jam’iyyar Labour Party (LP).

Shugaban jam'iyyar APC na jihar, Dakta Kingsley Ononogbu, a wata sanarwa da ya fitar sa'o'i kaɗan bayan hukuncin kotun, ya bayyana hukuncin a matsayin rashin adalci, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Ɗan Takarar PDP Da Kotu Ayyana a Matsayin Gwamnan Nasarawa

APC ta yi watsi da hukuncin zaben gwamnan Abia
APC za ta daukaka kara kan hukuncin zaben gwamnan jihar Abia Hoto: Alex Otti
Asali: Facebook

APC ta yi watsi da hukuncin kotu

Ononogbu ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta umurci tawagar lauyoyin ta da ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ta yanke.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Wannan hukunci da kotun mai alƙalai uku suka yanke, rashin adalci ne tsantsa. Ba za mu amince da shi ba kuma mun yi watsi da shi."
"Mun yi Allah wadai da hukuncin da kotun ta yanke ba tare da wata shakka ba, saboda haka, mun umarci tawagar lauyoyinmu da ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ta yanke."
"Da wannan hukuncin na kotun, a fili yake cewa an yi rashin adalci, fiye da haka, kuma abin damuwa shi ne cewa kotu na iya daina zama fatan da talaka ke da shi wajen samun adalci idan aka cigaba da rashin gaskiya."

INEC Ta Fasa Daukaka Kara

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Gwamnan APC A Jihar Arewa, Ta Bai Wa PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta janye ɗaukaka ƙarar ɗa ta yi kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano.

Hukumar INEC ta janye ɗaukaka ƙarar ne bayan da farko ta nemi ƙalubalantar hukuncin da kotun ta yanke, na ƙwace nasarar gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng