Kotun Zabe Ta Kori Karar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Otti na Abia

Kotun Zabe Ta Kori Karar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Otti na Abia

  • Jam'iyyar PDP ta sha kashi a ƙarar da ta shigar tare da ɗan takararta suna masu kalubalantar nasarar gwamna Otti na jihar Abiya
  • Yayin yanke hukunci ranar Jumu'a, Kotun zaɓe mai zama a Umuahia ta kori karar bisa rashin cancanta
  • Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta ayyana Alex Otti na jam'iyyar Labour Party a matsayin wanda ya lashe zaɓen 18 ga watan Maris

Jihar Abia - Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamna mai zama a Umuahia, babban birnin jihar Abiya ta kori ƙarar jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Chief Okey Ahiwe.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Kotun ta kori kararrakin waɗanda suka ƙalubalanci nasarar Gwamnan jihar Abiya, Alex Otti na Labour Party.

Gwamnan jihar Abia, Alex Otti.
Kotun Zabe Ta Kori Karar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Otti na Abia Hoto: Alex Otti
Asali: Facebook

Dukkan ƙorafe-ƙorafe uku da masu ƙara suka gabatar Kotun ta yi watsi da su bisa rashin cancanta, kana da yanke hukuncin tabbatar da nasarar gwamna Otti ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Bayyana Sahihin Dan Takarar Da Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kebbi

Korafe-korafen da PDP da ɗan takararta suka gabatar a gaban Kotun sun haɗa da, “Wanda ake kara bai cancanci tsayawa takara ba, bai samu rinjayen kuri’un halal ba, da kuma cewa an samu kura-kurai a zaben."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan korar karar, Kotun zaɓe ta tafi hutun mintuna 10 gabanin ta dawo ta ɗora kan ƙarar da ɗan takarar gwamna karkshin inuwar APC, Chief Ikechi Emenike, ya shigar.

Idan Kotun ta dawo wannan hutu ne ake sa ran zata yanke hukunci kan ƙarar da ɗan takarar APC ya ƙalubalanci zaɓen Gwamna Otti a ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Mai yiwuwa jam'iyyar PDP ta ɗaukaka ƙara

A nasa ɓangaren, Lauyan jam'iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna, Chukwuemeka Nworgu, ya gode wa Kotun kana ya roƙi a ba shi kwafin takardar hukuncin.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Gwamnonin Da Kotu Ka Iya Kora a Cikin Watan Oktoba Da Dalilai

A cewarsa, ta haka ne kaɗai waɗanda yake karewa za su nazari kana su yanke shawarar matakin da za su ɗauka na gaba, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Sakataren PDP Ya Maida Babbar Mota Ga Gwamnatin Sokoto

A wani labarin kuma Umar Bature, Sakataren tsare-tsaren jam'iyyar PDP ta ƙasa ya maida motar Tarakta ga gwamnatin jihar Sakkwato.

Ya ce tsohuwar gwamnatin Aminu Tambuwal da ta shuɗe ce ta ba shi hayar motar amma sai da ya mata gyara kafin ta fara aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262