Jam'iyyar APC Ta Caccaki Atiku Kan Takardun Karatun Tinubu
- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta caccaki Atiku Abubakar kan takardun bayanan karatun Shugaba Tinubu
- Sakataren watsa labaran jam'iyyar na ƙasa wanda ya yi caccakar, ya bayyana cewa Atiku ya gama cin lokacinsa a siyasa
- Felix Morka ya shawarci ɗan takarar shugaban ƙasan na PDP da ya daina wahalar da kansa wajen yin shari'a da Tinubu
FCT, Abuja - Sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya caccaki Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.
Atiku ya shigar da ƙara ne a wata kotun Amurka domin neman takardun bayanan karatun shugaban ƙasa Bola Tinubu, a jami'ar jihar Chicago.
Ya buƙaci samun takardun ne domin su goyi bayan zargin da yake yi na cewa Tinubu ya yi amfani da jabun satifiket na jami'ar CSU.
"Siyasar Atiku ta zo ƙarshe", Morka
Da yake tsokaci kan lamarin a lokacin da ya fito a shirin safe na gidan talabijin na ARISE TV, Morka ya bayyana Atiku a matsayin dan siyasa wanda komai ya tsaya masa cak, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce akwai buƙatar Atiku ya huta kan ƙarar da ya ke yi da shugaban ƙasa Tinubu.
A kalamansa:
"Sakamakon shari'ar da aka yi a Amurka dangane da wannan lamarin shi ne dai abin da muka yi hasashe kuma muka sani a tuntuni, wanda shi ne cewa shugaban ƙasan Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dalibin jami'ar jihar Chicago ne."
"Siyasar Atiku Abubakar ta tsaya cak. Komai ya ƙare masa. Kuma ina ganin ya kamata ya fahimci hakan. Ya yi wa ƙasar nan hidima a matsayin mataimakin shugaban ƙasa. Ya riƙe wasu muƙamai. Wannan ya isa duk wani ɗan siyasa a ƙasar nan. Na yaba da hidimarsa, amma yana buƙatar ya manta da wannan lamarin."
"Babu wani abu daga CSU wanda ya fara nuna cewa wannan shugaban ƙasan, a matsayinsa na ɗalibi da yanzu a matsayin shugaban ƙasa, ya yi wani abu na rashin gaskiya ko wanda zai kawo zargi dangane da iƙirarinsa na cewa ya kammala karatu a jami'ar CSU."
CSU Ta Tabbatar Da Ingancin Satifiket Din Tinubu
A wani labarin kuma, jami'ar jihar Chicago ta tabbatar da takardar shaidar kammala karatun da Shugaba Tinubu ya gabatarwa hukumar INEC.
Jami'ar ta bayyana cewa satifiket wanda Shugaba Tinubu ya samu bayan kammala karatunsa a jami'ar a shekarar 1979, mai inganci ne.
Asali: Legit.ng