Kotu Ta Tabbatar Da Nasir Idris a Matsayin Gwamnan Jihar Kebbi

Kotu Ta Tabbatar Da Nasir Idris a Matsayin Gwamnan Jihar Kebbi

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kebbi ta tabbatar da sahihancin zaɓen gwamna Nasir Idris na jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
  • Kotun zaɓen ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ɗan takararta, Aminu Bande suka shigar suna ƙalubalantar nasarar gwamnan
  • Hukumar zaɓe mai zaman ƙanta (INEC) ta sanar da gwamnan a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris

Jihar Kebbi - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kebbi, a ranar Alhami, 5 ga watan Oktoba, ta tabbatar da nasarar gwamna Nasir Idris, a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris.

Jaridar Vanguard ta ce kotun ta tabbatar da Nasir Idris a matsayin sahihin gwamnan jihar.

Kotu ta tabbatar da nasarar gwamna Nasir Idris
Kotu ta tabbatar da sahihancin zaben gwamna Nasir Idris Hoto: @NasirIdrisKG
Asali: Twitter

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ɗan takararta Aminu Bande sun ƙalubalanci nasarar da gwamnan da mataimakinsa suka samu a zaɓen ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Kotun Zaɓe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan LP a Zaben 2023

Kotun zaɓen a ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba, ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP ta shigar tare da tabbatar da nasarar Nasiru Idris na APC a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa kotun ta yi watsi da ƙarar?

A hukuncin da ya yanke wanda ya ɗauki tsawon sa'o'i 5, alƙalin kotun, mai shari'a Ofem I. Ofem ya bayyana cewa ƴan adawa sun kasa tabbatar da zargin yin amfani da takardun bogi, rahoton Tribune ya tabbatar.

Mai shari’a Ofem ya yi watsi da zargin ƙin yin murabus a matsayinsa na malami da gwamnan ya yi kafin ya tsaya takara, inda ya bayyana cewa hakan haƙƙin jam'iyyarsa ta yanke hukunci ba kotun zaɓe ba.

A dalilin hakan, sai ya yi watsi da ƙarar jam'iyyar PDP ɗan takararta na gwamna Manjo-Janar Aminu Bande, sannan ya tabbatar da nasarar jam’iyyar APC da ɗan takararta na gwamna.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Gwamnonin Da Kotu Ka Iya Kora a Cikin Watan Oktoba Da Dalilai

Wane fata ake yi wa gwamnan?

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani ɗan jihar Kebbi mai suna Idris Kamba, wanda ya nuna cewa tabbas gwamnan shi ya ci zaɓen da aka yi, kuma kotu ta yi adalci wajen tabbatar da nasarar.

Malam Idris ya yi fatan cewa gwamnan zai share musu hawayensu a jihar, inda ya bayyana cewa yanayin kamun ludayinsa ya nuna cewa talakawa za su ji daɗin mulkinsa.

Gwamnonin Da Ka Iya Rasa Kujerarsu

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotunan sauraron ƙararrakin zaɓukan gwamna na cigaba da yanke hukunci kan ƙararrakin da aka shigar a gabansu.

Ya zuwa gwamnoni takwas na jiran hukuncin da kotunan da ke sauraron ƙararrakin da aka shigar kan nasararsu, za su yanke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng