Abba Gida-Gida Ya Nada Sabbin Shugabanni 10 Na Wasu Hukumomi a Kano

Abba Gida-Gida Ya Nada Sabbin Shugabanni 10 Na Wasu Hukumomi a Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa sabbin shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin Kano guda 10
  • Sunayen waɗanda Allah ya bai wa muƙaman na ƙunshe ne a wata sanarwa da babban sakataren watsa labaran gwamna ya fitar
  • Ya buƙaci mutanen da aka naɗa su yi amfani da kwarewarsu wajen sauke nauyin amanar da aka ɗora musu

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ya amince da nadin shugabanni 10 a wasu ma'aikatun gwamnati a jihar.

Sabbin naɗe-naɗen da Abba Gida-Gida ya yi na ƙunshe ne a wata sanarwa da babban Sakataren watsa labaransa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a birnin Kano.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Abba Gida-Gida Ya Nada Sabbin Shugabanni 10 Na Wasu Hukumomi a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa an yi waɗan nan naɗe-naɗen ne a ƙoƙarin gwamnatinsa na lalubo mutane na gari domin inganta harkokin shugabanci, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Duk da Kotu Ta Tsige Shi, Abba Gida-Gida Ya Bada Hutun Kwana Ɗaya Na Murnar Haihuwar Annabi SAW

Gwamnan ya buƙaci waɗanda aka nada da su yi amfani da kwarewarsu wajen gudanar da ayyukansu ta yadda za su yi wa al’ummar jihar hidima da kuma sauke nauyin da aka ɗora musu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin waɗanda Abba Gida-Gida ya naɗa

A riwayar Punch, sanarwan ta jero sabbin shugabannin ma'aikatu, hukumomi da sashin gwamnati da aka naɗa, ga su kamar haka:

1. Salisu A. Kabo - Shugaban hukumar tallafa wa matasa

2. Dakta Hamisu Sadi Ali - Darakta Janar na ofishin kula da harkokin bashi

3. Abduljabbar Mohammed Umar - Shugaban hukumar zuba hannun jari (KAN-INVEST)

4. Yusuf Kabir Gaya - Shugaban hukumar ilimi a matakin farko (SUBEB)

5. Mustapha Adamu Indabawa - Shugaban gidan talabijin ɗin Rimi (ARTV)

6. Hamisu Dogon Nama - Shugaban kasuwar Kantin Kwari ta jihar Kano

7. Abdulkadir B. Hussain - Shugaban ƙasuwar Sabon gari

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Gida-Gida Ya Tuna Da Dalibai Mata, Ya Yi Musu Wani Babban Gata

8. Dakta Kabiru Sani Magashi - Muƙaddashin shugaban hukumar KASCO

9. Aminu Aminu Mai-Famfo - Mataimakin shugaban KASCO

10. Injiniya Abubakar Sadiq J. - Mataimakin shugaban Kano Line.

Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Dauki Nauyin Karatun Dalibai 870 a Jihar Kano

A wani rahoton kuma Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Jibrin Barau, ya cigaba da daukar dawainiyar wasu daga cikin daliban jihar Kano.

Sanatan ya ba mutanen Arewacin jihar Kano tallafin N20, 000 domin yin karatu a jami’ar nan ta Yusuf Maitama Sule da ake kira North West.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262