Ganduje Ya Yi Alkawarin Dawo da Martabar Siyasar Kano Idan APC Ta Karbi Mulki
- Shugaban jam’iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya yi wa ‘yan kasuwar jihar Kano alkawarin dawo da martabar kasuwanci
- Ganduje ya bayyana haka ne a yau Talata 3 ga watan Oktoba yayin karbar bakwancin shugabannin ‘yan kasuwa daga Kano
- Ya ce dawowar APC ce kadai zai dawo da martabar siyasar jihar Kano a idon duniya da sauran jama’a
Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Abdullahi Ganduje ya yi wa ‘yan jihar alkawarin kawo sauyi kan rusau.
Ganduje ya bayyana haka yayin da ya karbi bakwancin ‘yan kasuwa daga jihar Kano a ofishinsa da ke Abuja a yau Talata 3 ga watan Oktoba.
Wane alkawari Ganduje ya yi wa 'yan kasuwar Kano?
Ya musu alkawarin cewa da zarar jam’iyyarsu ta karbi mulki za su dai-dai ta komai kamar yadda su ke a baya, The Nation ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Abin takaici ne kan matsalar da ku ka taso da ita, wannan matsalar rushe-rushe ba bisa ka’ida ba abin bakin ciki ne.
“Sun lalata tattalin arziki da kasuwancin mutanen jihar Kano wannan abin takaici ne.
“Mutane da dama sun fara tunanin kin zuwa Kano don yin kasuwanci, har bankuna ba sa karbar takardar shaidar wurin zama saboda tsoron kada a kwace takardar.”
Meye martanin 'yan kasuwar da ke Kano?
Ganduje ya ce ya taya wadanda su ka dauki matakin zuwa kotu inda ya ce rusau din ya yi muni yadda har ya gurgunta tattalin arziki.
Ya kara da cewa a yanzu kotu ta fara daukar mataki kan gwamnati na biyan kudaden diyya wanda hakan abin yabawa ne, Head Topics ta tattaro.
Ya ce abu daya ne kadai zai gyara siyasar Kano shi ne dawowar APC mulkin jihar inda ya ce su na kan hanya.
A martaninshi, shugaban ‘yan kasuwar, Umar Ladiyo ya bayyana irin halin da su ka shiga dalilin rusau a jihar.
Ya ce sun yi murna kwarai da hukuncin kotu da ta dawo da Gawuna a matsayin halastaccen zababben gwamna a jihar.
Sule zai daukaka kara kan hukuncin kotu
A wani labarin, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce zai daukaka kara kan hukuncin kotun zabe.
Sule ya bayyana haka ne bayan kotun zabe ta kwace kujerarshi tare da bai wa dan takarar PDP.
Asali: Legit.ng