Jigon PDP, Reno Omokri Ya Soki Peter Obi Kan kin Bayyana Digiri Dinsa Ga INEC
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya sha suka bayan hira da gidan talabijin na Arise
- Jigon jam'iyyar PDP, Reno Omokri ya caccaki Peter Obi kan shaidar takardun karatunsa bayan Atiku ya samu damar ganin takardun Tinubu
- Omokri ya tambayi Obi dalillin kin mika takardar kammala digiri dinsa ga hukumar zabe ta INEC lokacin zaben shugaban kasa
FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar PDP, Reno Omokri ya yi martani ga dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi.
Omokri wanda tsohon hadimin shugaban kasa ne ya bukaci Peter Obi ya bayyana takardar shaidar kammala digiri dinsa, Legit ta tattaro.
Meye Reno ke cewa kan takardun Peter Obi?
Reno ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Talata 3 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce me yasa Obi bai mika takardar shaidar kammala digiri dinsa ba na Jami'ar Najeriya ta Nsukka.
Wannan na zuwa ne yayin da Jami'ar Chicago ta turawa Atiku Abubakar wasu daga cikin takardun Bola Tinubu bayan ya bukaci hakan.
Yadda Omokri ya soki Peter Obi kan takardun Tinubu
Yayin da ya ke caccakar hirar da Obi ya yi, Omokri ya ce:
"Peter Obi, Jami'ar Chicago ta tabbatar da takardar shaidar karatun Tinubu da kuma ingancinsu, sai jiya da safe ka ke hira da gidan talabijin na Arise kan cewa takardun Tinubu jabu ne.
"Yanzu ka amsa wannan tambaya, me yasa ba ka mika takardar shaidar kammala digiri din ka ba ga hukumar zabe ta INEC?
Wannan martani na Omokri na zuwa ne bayan Atiku Abubakar ya samu shaidar takardun karatun Shugaba Bola Tinubu daga Jami'ar Chicago da ke Amurka.
Atiku Abubakar na kalubalantar zaben Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a jam'iyyar APC.
Atiku ya samo takardun karatun Tinubu
A wani labarin, Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya lalubo takardun karatun Tinubu.
Atiku ya shigar da kara kan zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Faburairu na wannan shekara.
A watan Satumba ne kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa ta tabbatar da Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya.
Asali: Legit.ng