Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Wanda Kotu Ta Ce Ya Ci Zaben Nasarawa
- Kotun zaɓe ta bayyana ɗan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Nasarawa a watan Maris
- Alƙalan Kotun sun sauke gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC daga matsayin gwamna ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba
- Mun tattaro muku muhimman abubuwa game da Ombugadu, wanda Kotu ta ce shi ya ci zaɓen jihar Nasarawa
Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben Gwamnan jihar Nasarawa ta ayyana ɗan takarar PDP, David Ombugadu, a matsayin sahihin wanda ya ci zaɓen gwamna a watan Maris.
Kotun ta a bayyana haka ne yayin zaman yanke hukunci ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba, 2023, inda ta tsige Abdullahi Sule na jam'iyyar APC daga kujerar gwamnan Nasarawa.
Daily Trust ta rawaito cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Gwamna Sule a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Bayan sanar da haka ne, Mista Ombugadu ya garzaya kotun zaɓen kuma ya shigar da karar kalubalantar nasarar abokin hamayyarsa na APC, Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da yake karanto hukunci, shugaban kwamitin alkalan Kotun, mai shari'a Ezekiel Ajayi, ya bayyana Emmanuel Ombugadu na PDP a matsayin sahihin gwamnan jihar Nasarawa.
Jerin muhimman abubuwa 6 game da Ombugadu
1. An haifi Mista Ombugadu a ranar 10 ga watan Janairu, 1978
2. Ya yi karatun Firamare a makarantar LEA Primary School da ke Kakuri a cikin jihar Kaduna
3. A 2001, ya samu shaidar kammala karatun digiri na farko (Bsc.) a fannin tattalin arziki (Economics), daga Jami'ar Jos
4. Daga nan ya wuce aikin bautar ƙasa watau NYSC a shekarar 2003. Bayan haka ya ci gaba da karatun digiri na biyu a jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Ribas
5. Ombugadu ya riƙe kujerar ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Akwanga, Wamba da Nasarawa Eggon daga 2011 zuwa 2019.
6. Ya tsaya takarar gwamnan jihar Nasarawa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben 2019.
Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Fubara Na Jihar Ribas
A wani rahoton kuma Kotun zabe ta sanar da hukuncin da ta yanke kan karar da ɗan takarar LP ya kalubalanci nasarar gwamna Fubara na jihar Ribas.
A zaman yanke hukunci ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba, Kotun ta kori ƙarar bisa rashin cancanta da gaza tabbatar da zargi.
Asali: Legit.ng